✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barayin daji sun sa mutum 7,000 hijira a Sakkwato

Masu gudun hijirar sun koma wurin abokan arziki da sansanonin da aka tanadar.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta ce mutum dubu bakwai ne suka tsere daga muhallansu sakamakon hare-haren barayin daji a kananan hukumomi biyu a Jihar Sakkwato. 

Babban Jami’in Hulda da Jama’a na NEMA, Manzo Ezekiel, ya bayyana cewa kananan hukumomin su ne: Sabon Birni da Isa.

A cewarsa, Hukumar da takwararta a Jihar Sakkwato (SEMA) sun yi ittifaki kan alkaluman kididdigar da suka yi cewa akalla mutum 6,200 da lamarin ya shafa ne suke gudun hijira a sansanoni da gidajen ’yan uwa. 

Sansanonin suna a makarantar firamare ta Sabon Birni da cikin garin Isa a Jihar Sakkwaton sai kuma a garin Shinkafi mai makwabtaka da ke cikin Jihar Zamfara.

Aliyu Kafindangi, wanda shi ne Babban Jami’in NEMA a jihar, wanda ya jagoranci kididdigar alkaluman ya jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, sannan ya ba su tabbacin samar musu da tallafin da ya dace. 

Sai dai ya ce saboda tabarbarewar yanayin tsaro, ayarin hukumar bai iya samun sukunin shiga yankunan a kan lokaci ba, domin duba halin da suka samu kansu ciki.