✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayi sun kashe dan acaba, sun tafi da babur dinsa

Barayin sun yanka wuyansa sannan suka yi awon gaba da babur dinsa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ce wasu da ake zargin barayi ne sun kashe wani matashi dan acaba mai shekara 23 a Karamar Hukumar Birnikudu ta jihar.

Kakakin rundunar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Dutse.

“Da misalin karfe 8:20 na safe, an tsinci gawar wani dan acaba, Umar Abubakar, mai shekara 23 a kauyen Lutai, Karamar Hukumar Birnikudu, a cikin daji tsakanin garin Babaldu da kauyen Bakatuma.

“Mai babur din ya dauki fasinjojin da ba a san ko su waye ba daga Babaldu a cikin dare, da suka isa daji kafin kauyen Bakatuma, sai suka yanka wuyansa da wani abu mai kaifi.

“Ya mutu nan take kuma barayin sun tafi da babur dinsa,” inji shi.

Shiisu, ya ce marigayin dan kauyen Lautai, an tsinci gawarsa ne a ranar Juma’a da misalin karfe 8:20 na safe a cikin daji.

Kakakin ya ce ’yan sanda sun ziyarci wurin da abin ya faru, kuma sun dauke gawar zuwa Babban Asibitin Birninkudu don yin bincike.

A cewarsa, ’yan sanda sun shiga farauta don cafke wadanda suka aikata laifin.