A makon jiya ne wadansu da ake zargin barayi ne dauke da miyagun makamai suka kai hari a Sakatariyar Karamar Hukumar Auyo da ke Jihar Jigawa, inda suka daure biyu daga cikin masu gadin sakatariyar, sauran masu gadin suka tsere.
Rahotannin da Aminiya ta samu sun nuna cewa ana zaton barayin sun biyo sawun wasu kudi ne da karamar hukumar ta amso daga banki domin biyan wadansu ma’aikata hakkokinsu.Bayan barayin sun balle dukan ofisoshin da suke zaton an ajiye kudin ciki har da ofishin Ma’ajin Karamar Hukumar, ba su samu komai ba face Naira dubu 50, inji majyarmu.
Rahotannin sun ce barayin sun awon gaba da akwatunan talabijin kirar Plasma guda uku da na’urar kwamfuta, inda suka bar masu gadin a daure cikin wani daki, sai da ma’aikata suka fito aiki ne da safe aka kwance su.
Wani mazaunin garin Auyo da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce, “Kudi ne karamar hukumar ta amso daga banki don biyan ma’aikata, amma da magariba ta yi aka ajiye kudin da nufin sai washegari a karasa biya, shi ne barayin suka kawo hari. Amma an ce ba su tarar da kudin ba.”
Babban Jami’in Watsa Labarai na Karamar Hukumar, Malam Sani Adamu Sarawa ya tabbacin da kai harin, inda ya ce ’yan sanda sun kama masu gadin, domin su amsa tambayoyi, kuma ya musanta cewa an saci kudi daga karamar hukumar, ya ce ya tabbatar da sace talabijin.
Ya ce har zuwa lokacin ba a kiyasta kudin kayan da barayin suka sata ba, inda ya tabbatar da cewa barayin sun daure masu gadin kuma sun yi amfani da wasu manyan kwaduna suka garkame kofar shiga sakatariyar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce barayin ba su dauki komai ba, sai Naira dubu 50, ita ma sun same ta ce a wani ofishi, hakan ya biyo bayan canja shawarar da wanda kudin ke wajensa ya yi ne, na kin ajiye kudin a ofishinsa.
Jinjiri ya ce an samu masu gadin a daure a wani daki, kuma yanzu haka masu gadin suna wajensu suna amsa tambayoyi, amma ya ce da zarar sun kammala bincikensu, za su gurfanar da su ne a gaban kotu, domin ci gaba da bincike da hukunta su.