✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayi sun fasa ofishin Media Trust dake Kaduna

Barayin sun fasa ofishin, tare da sace kayan Daraktan Media Trust da ya rasu a satin da ya wuce.

Wasu bata gari sun fasa ofishin kamfani Media Trust dake wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a garin Kaduna sannan suka sace muhimman kayayyaki a ciki.

Wani mai gadi dake makwabtaka da ofishin mai suna Adamu ya bayyana cewa barayin sun sami nasarar kwashe muhimman kayayyaki daga ofishin.

Kayayyakin da bata garin suka sata wadanda suke a ofishi Daraktan kamfanin ne, Rabi’u Garba wanda ya rasu a makon da ya gabata a asibiti a kasar Masar

“Lokacin da muka isa wurin mun iske mai gadin wurin a daure jini na zuba daga kansa, kuma an masa raunuka a jikinsa,” in ji Adamu.

Aminiya ta gano cewa barayin sun fasa ofishin, tare da sace na’ura mai kwakwalwa da wasu muhimman kayayyakin amfani na kamfanin dake kan titin Mogadishu a garin Kaduna.

Barayin sun yi wa mai gadin wajen dukan kawo wuka kafin daga bisani suka daure shi.

Bincike ya gano cewa barayin sun yashe ofishin, sun kwashi talabijin, na’ura mai kwakwalwa, da sauran kayan amfanin ofishin.