Kudurin neman kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC), wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya gabatar, ya tsallake karatu na farko a Majalisar.
Kudurin mai taken, bukatar kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma, 2023, ya tsallake karatu na farko ne a zaman majalisar na ranar Talata wanda aka yi a karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
- Shugaban Amurka ya naɗa ’yan Najeriya 2 a matsayin mashawarta
- Shekara 13 ke nan rabon da a yi wa ’yan majalisa karin kasafin kudi – Abbas
Akawun Majalisar Dattawa, Barista Chinedu Akubueze ne ya karanta taken kudurin a takaice a lokacin zaman.
A wata sanarwa daga sashen yada labarai na ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar, an bayyana cewa idan aka kafa hukumar, za ta taimaka wajen kawo ci gaban yankin na Arewa maso Yamma mai jihohi bakwai; Kano, Kaduna, Kebbi, Katsina, Jigawa, Sokoto da Zamfara.
Haka kuma, idan aka kafa ta, hukumar za ta samo kudaden da za ta yi amfani da su wajen inganta harkokin noma da kasuwanci a yankin.
A shekara 10 da suka gabata, yankin na Arewa maso Yamma, musamman jihohin Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara sun sha fama da matsalar rashin tsaro, wanda hakan ya taimaka wajen kawo tsaiko ga ci gaban yankin.
Idan aka kafa hukumar, za ta fi mayar da hankali wajen samar da ci gaban yankin na Arewa maso Yamma, musamman a bangaren noma da kiwo, samar da gidaje, raya karkara, samar da wutar lantarki da ruwan sha da bunkasar kasuwanci.
Da sannu za a gabatar da kudurin domin karatu na biyu.