✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 13 ke nan rabon da a yi wa ’yan majalisa karin kasafin kudi – Abbas

Ya ce duk da tashin farashin kayayyaki, ba a kara musu kudin kasafin ba

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya ce shekara 13 ke nan rabon da a kara kasafin kudin Majalisar Dokoki ta Kasa duk da tashin farashin kayayyaki.

A cewar Musa Abdullahi Krishi, mai magana da yawun Kakakin, Abbas ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Gamayyar ’Yan Kasuwar Afirka a Abuja ranar Laraba.

Ya ce, “Kudaden da ake kashewa sun tashi sosai, amma kasafin kudinmu bai karu ba a cikin wadannan shekarun.

“A zahirin gaskiya ma, akwai lokacin da sai da aka rage kasafin a shekara ta 2011,” kamar yadda Kakakin ya shaida wa Babban Daraktan gamayyar, Dotun Ajayi.

Abbas ya kuma shaida musu cewa majalisa ta 10 mai ci ta kirkiri kwamitoci kusan guda 60 a kokarinta na inganta kawance tsakaninta da sauran majalisu a fadin duniya.

Kakakin ya ce ana bukatar kawancen ne domin karfafa aikin ’yan majalisar, inda ya ce kofarsu a bude take ga duk wanda zai inganta wannan kawancen.

“Ko a makonni biyu da suka gabata, sai da irin waɗannan kwamitocin suka ƙaru daga 43 zuwa 65. Jiya-jiyan nan ma mun kara wani daga kasar Serbia, inda suka koma 66 ke nan,” in ji Abbas.