Daga Hudubar Hasan bin Abdul’aziz Alu Assheikh
Masallacin Annabi, Madina
Fassarar Salihu Makera
Huduba ta farko
Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa datarwarSa da ni’imominSa. Na shaida babu wanda ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, girmamawa ga sha’aninSa. Kuma na shaida Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci da albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa da ’yan uwansa.
Bayan haka, ya ’yan uwa a cikin Musulunci! Me ya kai darare da ranaku saurin wucewa? Me ya kai watanni da shekaru saurin shudewa? Haka halin duniya yake, mai saurin gushewa ne, yanzu za ta basar da mutum, halinta ba mai tabbata ba ne, kuma zukatan mutanen kwarai ba masu natsuwa da ita ba ne. Wannan Sunnar Allah ce game da halittarSa, zamunna da al’amura suna gudana ne a kan wani ajali na musamman “Ga kowane ajali akwai littafi (hukunci) iyakantacce.” (K:13:38).
Lallai masu tunani da hankali da basira da hangen nesa sukan hango wadannan abubuwa cikakkiyar hangowa. Sai su rika lura da abin da zai zo a karshe, su rika taka-tsantsan da yadda duniya take sauri da gudu, domin ya zame musu abin gargadi. Allah Madaukaki Yana cewa: “Lallai ne a cikin halittar sammai da kasa da sassavawar dare da wuni akwai ayoyi ga ma’abuta hankali.” (K:3:190).
Ya al’ummar Musulmi! Kwanan nan muke maraba da Ramadan, ga shi muna yin ban kwana da shi, kamar kiftawar ido, wane irin sauri ne haka? Wane irin gudu ne haka? Godiya ta tabbata ga Allah kan abin da Ya hukunta kuma Ya gudanar, muna yi maSa shukura bisa abin da Ya bayar kuma Ya ni’imtar. Hakika wanda ya ci riba, ya ci, wanda kuma ya yi asara ya yi a cikin Ramadan, “Lallai ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya samu babban rabo. Kuma lallai ne wanda ya tubude shi (da laifi) ya tave.” (K:91:9-10).
Azumi yana ta wucewa, ya juya baya, ya tafi da irin ayyukanku, yana mai bayar da shaida kan abin kuka yi a cikinsa. Ku tambayin kawunanku shin ya tafi ne da abin godiyarku ko kuwa da abin kaiton da kuka yi ya tafi? Duk wanda ya kyautata, to, ya ci gaba da kyautatawar, wanda ya gaza, to ya sake salon tafiya!
Ya ’yan uwa a Musulunci! Ba abin da ya saura ga al’umma face ta rika yi wa kanta hisabi a kullum, ta tabbata ga kiyaye dokokin Allah. Babu abin da ya kamace ta, kamar yawaita tunani da nazari kan al’amura da sha’anonin da suka shafi rayuwa da mutuwa da halayen da ake ciki. Ta kalli abubuwa da karshensu, ta kalli yadda komai ke tafiya daki-daki, ta dubi abin da ke faruwa, don ya zame mata aya game da yau da gobenta.
Lallai a cikin watan Ramadan da yake shudewa akwai wasu al’amura da suka wajaba a kan al’umma, wadanda ake shugabanta da shugabanni, su rike su a matsayin gadoji na kaiwa ga nasara. Su rike su don kyautata abubuwan da suka lalace, kafin lokaci ya kuvuce musu, ko zamani ya juya!
Lallai a cikin Ramadan akwai kyaututtuka masu yawa da darussa masu girma da suka wajaba wannan al’umma ta tabbatar da su wajen yaki da Shaidan. Ta rike su don samun kyakkyawar tafiya a tafarki madaidaici, ta yi amfani da su domin ganin bayan kowace cuta da fasadi.
Ya bayin Allah! Lallai shari’ar Musulunci tana kunshe da wadansu sirrurrka da ba su kirguwa da manufofi masu daraja. Yana daga cikin manufar azumi, ya zama hanya mai girma ta gina dabi’ar takawa a tsakanin Musulmi. Takawa a yalwatacciyar ma’anarta da surarta, don haka ya kai Musulmi! Ka dauki azumin da ka yi, ya zama makaranta da ka samu horon yin abin da ya dace da kuma karfin hali wajen aikata alheri da juriya wajen yaki da son zuciya da sha’awoyi. Ka dauki azumin da ka yi a matsayin tsarkake zahiri da badininka da tsabtace ayyuka da zuciyarka, zuciyarka ta zama a kan hanya madaidaiciya, a kullum cikin karfin jiki babu rauni, ta zamo mai kazar-kazar a bisa kyauta yi, babu abin da ke yi mata shamaki. Ka yi dubi shin kana gyara abin da ya vaci da mikar da abin da ya karkace da karfafa abin da ya yi rauni daga abin da ya shafi gyara da alheri da shiriya ko a’a? “Kuma ku yi jihadi a cikin (al’amarin) Allah, hakikanin jihadinSa…” (K:22:78).
Dan uwa Musulmi! Idan kana bibiyar Alkur’ani, za ka ga kiraye-kirayensa a kan tsayuwa wajen aikata alheri da tabbatuwa a kan shiriya, Allah Madaukaki Yana cewa: “Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da wadanda suka tuba tare da kai, kuna ba masu ketare haddi ba.” (K:11:112). Da kuma fadinSa: “Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.” (K:15:99). Wannan wasiyya ta Ubangiji an yi wa mutane ne domin tsara yadda za su kasance tare da dauwama a kan al’amuran Musulunci da yin abubuwa bisa ka’idar addini da tsayuwa a inda ya ce a tsaya da bin umarninsa da hanuwa daga abin da ya hana a bisa fuskar kamala da hanya mikakkiya.
Saurari hasken Annabta (SAW) yana takaita maka wannan wasiyya mai girma ma’abuciyar ibarori masu kyau da ma’ana mai daraja, gajerar kalma mai ishara da yawa, ita ce wasiyyar da Manzonmu (SAW) ya yi ga al’umma baki daya, wasiyyar da take nuni da riko da imani cikakke da lizimtar akida sahihiya da hakuri a bisa ayyukan da’a da guje wa ayyukan da aka hana da bin kyawawan halaye da mu’amala mai kyau. Yana cewa da mutumin da ya ce masa: “Ka fada min wata magana a cikin Musulunci, maganar da ba zan sake tambayar wani a kanta ba a bayanka.” Sai (SAW) ya ce: “Ka ce: “Na yi imani da Allah,” sannan ka daidaita (ka tsayu a kan haka).”
Lallai wannan wasiyya ce – bisa izinin Allah – da ta kunshi al’amura masu yawa, ta kunshi rayuwa mai kyau yardajjiya da take tabbatar wa muminai kyakkyawar rayuwa ta har abada da akiba amintacciya. “Lallai ne wadanda suka ce “Ubangijinmu Allah ne,” sa’an nan suka daidaitu, to, babu wani abin tsoro a kansu, kuma ba za su yi bakin ciki ba. Wadannan ’yan Aljanna ne, suna madauwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance suna aikatawa.” (K:46:13-14).