’Yan jarida a jihar Binuwai sun yi tir da cin zarafin da tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama na Najeriya Femi Fani-Kayode ya yi wa takwaransu.
A ranar Talata ne dai wani bidiyo ya karade gari inda aka jiyo Mista Femi yana zage-zage kan wata tambaya da dan jaridar da ke aiki da kamfanin Daily Trust a Kalaba, yayin wani taron manema labarai.
Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) reshen jihar Binuwai ta soki abin da Fani-Kayoden ya yi a jawabin bayan taronta dauke dasa hannun shugaban kwamitin taron, Mista Terna Uma da sakatarensa Mista Sam Tyav a garin Makurdi.
“Reshen ya bi sahun uwar kungiya ta kasa wajen yin Allah-wadai da cin zarafin da Femi Fani-Kayode ya yi wa wakilin jaridar Daily Trust a a kan kawai ya yi masa tambaya.
“Muna bayyanawa karara cewa ba za mu lamunci cin zarafi ko wulakanta dan jarida ba lokacin da yake kan ganiyar aikinsa ta kowace fuska ba”, sanarwar.
Sannan ta yi kira ga Gwamantin Tarayya ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a kasa, musamman a Kudancin Kaduna inda rikici ya ki ci ya ki cinyewa.
‘Yan jaridar sun kuma lura cewa kalubalen tsaron da ke kara ta’azzara na dada zama abin damuwa musamman a garin Makurdi da kauyukan da ke da makwabtaka da shi, da hanyar Makurdi-Aliade da yanzu ba ta biyuwa da daddare.