Ranar Juma’a 21 ga Satumba da tsakar rana na samu sakon waya daga Sashen Sadarwa na Babban Bankin Najeriya (CBN) cewa Gwamnan Bankin CBN, Godwin Emefiele yana gayyatata taron manema labarai da misalin karfe uku na yamma a ranar a ofishinsu da ke Ikko. Harajin da sashen da ke kula da bankuna ya sanya wa wasu bankuna da ya kai Naira biliyan biyar tuni ya game kafafen watsa labarai saboda haka na yi tsammanin bankin zai yi wata babbar sanarwa a kan haka.
Na isa harabar Bankin CBN tare da abokan aikina manema labarai a bangaren kudi da tattalin arziki, muna ta mamakin abin da zai faru. Muna ta labarin abubwan da suka faru a wuraren da muka ziyarta a baya, sai aka gaya mana cewa mu jira Gwamnan Bankin yana wani muhimmin taro.
Bayan karfe bakwai da ’yan mintina sai aka jagorance mu zuwa dakin taron, muka ga Manajan Daraktan Hukumar Tattala Kadara ta Najeriya, Ahmed Kuru a zaune, a gefensa akwai Manajan Darakta kuma Babban Jami’i na Hukumar Kare Masu Ajiya a Banki, Umaru Ibrahim, sai kawai muka zauna muna mamaki.
Nan da nan aka fara taron, kamar likita da yake son yi wa ’yan uwan marar lafiya jawabi, sai ya gaya mana cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye lasisin da ya bai wa Bankin Skye.
Sai zuciyata ta fara bugawa daga dakika 20 zuwa 120, sai kawai na fara bude asusuna na Bankin Skye ta yanar gizo don in kwashe ’yan kudin da nake da su zuwa wani asusun ajiya na wani bankin kafin a kare taron kuma kafin a bayyana wa al’umma.
Sai Godwin Emefiele ya bayyana cewa “Bayan tattaunawa da Hukumar Kare Masu Ajiya a Bankuna ta NDIC, Bankin CBN ya yanke shawarar kafa Bankin Polaris don ya karbe kadarorin Bankin Skye.”
Ya kara da cewa “Daga yanzu dukan masu hulda da Bankin Skye sun zama abokan huldar sabon bankin kuma sabon Bankin Polaris ya saye asusun ajiyarsu da bayanansu.”
Sai kawai na ji na samu sa’ida cikin gaggawa. Hannuwana tuni suka fara gumi saboda kokarin da na rika yi na kwashe kudina daga Bankin Skye zuwa wani banki da wayata ta salula, sai kawai na ci gaba da tura kudin wani asusu don na riga na gaskata abin da Mista Emefiele ya fadi kuma don ya zama hankalina ya kwanta.
Ana buga labarin a kafar yanar gizo ta jaridarmu ta Daily Trust cikin minti biyar sai na fara samun kira daga jama’ar da suke son su kwashe kudinsu su tura wasu asusun ajiyar a wasu bankunan daga manema labarai da masu ruwa-da-tsaki a harkar banki tunda tuni labarin ya bazu.
Duk wanda yake da asusun ajiya a Bankin Skye yana da labarin fadi saboda yadda bankuna ke da alaka da tattalin arziki da kuma rayuwar al’umma na kowace kasa, shi ya sa rugujewar duk wani banki tana shafar al’amura ya fi ma a ce kasuwancin mutum ne ya ruguje kamar yadda kafar sadarwa ta Wikipedia ta fada.
Bankuna su ke bunkasa tattalin arziki da dorewarsa da samar da ayyuka da bunkasa arzikin kasa na kowace kasa da taimaka wa masu zuba hannun jari samun jari da taimaka wa kanana da matsakaitan kamfanoni da samar da bashi uwa uba kuma da tattala kudi.