Bankin katar National Bank (kNB) ya kara sayen hannun jari kashi 11 cikin 100 na Bankin Eco, a wata hada-hadar ciniki da aka kulla ta Dala miliyan 283, wannan al’amari ya kara sanya Bankin kNB ya zama mafi yawan hannun jari a wannan babban banki na Afirka.
A halin yanzu, kNB ya mallaki hannun jari har guda biliyan biyu da miliyan 80, inda yawan hannun jarin kNB idan aka tattara ya zama kashi 23 da rabi cikin 100, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwa.
Wannan cinikin dai an gudanar da shi a ranar Talatar da ta wuce bayan da kNB ya mallaki kasha 12 da rabi cikin 100 na hannun jarin wani banki da ke da “matsala” daga hannubn Kamafnin Ririta Asarar Hada-hadar Kasuwanci na AMCON, tumn a ranar 4 ga Satumbar 2014.
“Wannan na nuni da cewa bankin kNB ya zama mafi yawna hannun jari, inda kuma alakar bankin da Eco ya kara karfafa,” a cewar sanarwar da kNB ya bayar, inda ya bayyana cewa, wannan wata shawara ce da sashen saka jari na banki da Mongan Stanley suka bayar.
Bankin kNB, ya bayyana aniyarsa ta zama giwar bankuna a Gabas-ta-Tsakiya da nahiyar Afirka da nan da shekara ta 2017. Domin a halin yanzu shi ne banki na biyu a yawan dukiya baya ga Bankin Standard na Afirka ta Kudu.
Wannan jarin da aka zuba bankin Eco, shi ne karo na biyu da bankin katar ya sayi hannun jari a Afirka cikin shekara biyu. A Maris din 2013, ya saye harkokin kasuwan Societe Generale na Masar, a kan kudi Dala miliyan biyu, kuma bankin yana da rassa a kasashen da suka hada da Libiya da Mauritaniya da Kudnacin Sudan da Sudan da Tunusiyya.
Kamfanin ririta Asara na Najeriya (AMCON) shi ya mallaki hannun jarin bankin Eco a lokacin da bankin giwar Afirka yah ade da bankin Oceanic, wanda ya rushe, kuma AMCON ya tallafa masa da jari.
Shi kuwa mai Magana da yawun Bankin Eco, Richard Uku ya tabbatar da cewa an sayar da hannun jari mallakin Kamfanin ririta Asarar hada-hadar kasuwanci na Najeriya (AMCON) da ke cikin bankinsa. Ya ce, kNB shi ne mafi yawan jari na biyu a wannan babban banki a fadin Afirka, baya ga kamfanin saka jari na kasar AFirka ta Kudu.
“Wannan ciniki da aka kulla, ya fi karfin a ce bankin katar na da mafi yawan hannun jari a bankin Eco. Muna ma hankoron ganin dimbin kudi daga Gabas-ta-Tsakiya na shiga hada-hadar bankunahn Afirka,” a cewar Akinbamidele Akintola, Babban Jamiin Hada-hadar hannayen jari ta Afirka na Renaissance Capital.
Shi kuwa baban jami’in sarrafa kudi na bankin katar, Ramzi Mari, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters a Fabrairun bana, cewa, suna kokarin mallakar wasu bankunan a kasar Turkiyya da Maroko da kasashen yankin Saharar Afirka.
Masu bayar da bashi ’yan kasashen waje na sha’awar shigowa a dama da su wajen bunkasar kasuwanci a Afirka, saboda an gano, a kalla kasa da kashi daya bisa ukun ’yan Afirka ke da asusun ajiya a banki, sannan kasa da wannan adadi na kamfanoni ke bayarwa ko karbo rance.
Sannan akwai dimbin damar gudanar da hada-hadar kasuwanci, wadda ba a amfani da ita, inda ake has ashen samun dimbin riba, a wajen karba da bayar da bashi na fiye da kashi 10 cikin 100 a kasashe da dama, in an kwatanta da kasha biyu cikin 100 ko kasa da haka a kasashen Turai da dama.
Bankin Eco da Jihar Legas ta tallata shi, yana da rassa a kasashen Afirka 36, sannan ana sa ran karuwar yawan kudin hada-hadarsa da kashi 18.7 cikin 100 na kadarori nan da karshen shekarar 2014, inda zai daga daga kashi 17.5 cikin 100 da ke das hi tun a farkon rabin shekarar, a cewar Shugaban Bankin Albert Essien.
Mafi karancin jarin hada-hada a Najeriya bai wuce kashi 16 cikin 100 ba
Essien, ya ce, a karshen watan da ya wuce, ya yi hasashen Bankin Nedbank na Afirka ta Kudu zai narkar da bashin Dala miliyan 285 zuwa bashi a bankin Eco nan da karshen wannan shekarar, sannan ya kara hannun jarinsa da wata Dala miliyan 206, al’amarin da zai ba shi damar mallakar kashi 20 cikin 100 na hannayen jarin bankin Eco.
Bankin katar ya mallaki mafi yawan hannun jarin bankin Eco