Bankin Duniya ya ba kasar Gambiya tallafin Dalar Amurka miliyan 68 domin ta farfado da harkar yawon bude ido a cikinta.
Bangarorin biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar bayar da tallafin ranar Talata, yayin wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a Banjul, babban birnin kasar.
- ‘Yan bindiga sun yi wa ‘yan mata masu yi wa kasa hidima fyade
- LABARAN AMINIYA: Buhari Zai Tafi Senegal Jim Kadan Bayan Harin Kuje
Ana sa ran kasar za ta yi amfani da tallafin wajen farfado da bangaren da yake fuskantar barazanar sauyin yanayi, musamman ta gefen gabar tekun kasar.
Kasar ta Gambiya dai na mutane kimanin miliyan 21.
Kamar sauran bangarori a kasashen Afirka da dama, harkar yawon bude ido ta fuskanci mummunan kalubale sakamakon annobar COVID-19 da kuma yakin Ukraine, kamar yadda Manajan Daraktan Bankin Duniya mai kula da bangaren ayyuka, Axel Van Trotsenburg, ya bayyana.
Bangaren yawon bude ido dai na taimaka wa da kusan kaso 20 cikin 100 na kudaden da ake juyawa a kasar, kuma shi ne bangaren tattalin arzikin da ya fi kawo mata kudaden shiga.
Bankin na Duniya dai ya ce a shekarar 2020, annobar COVID-19 ta rage yawan tattalin arzikin kasar da kaso 0.2.
Sai dai tuni tattalin arzikin ya soma farfadowa, inda ya kai kusan kaso 5.6 a shekarar 2021, galibi daga irin kudaden da ake samu daga masu zuwa yawon bude idon, musamman a gabar teku.