✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin Duniya ya hana Uganda bashi saboda kin amincewa da auren jinsi daya

Shugaban Kasar, Yowere Moseveni ya yi Allah wadai da matakin

Bankin Duniya ya dakatar da shirin ba kasar Uganda rance saboda ta ki amincewa da kudurin dokar da ta halasta auren jinsi daya.

Shugaban Kasar, Yoweri Museveni dai ya bayyana matakin a matsayin yunkurin amfani da karfin tuwo don tilasta kasar ta amince da dokar.

Kasar dai ta kafa dokar da ake ganin tana daya daga cikin wadanda suka fi tsanani da ke yakar dokar auren jinsi dayan, wacce ta ce sam ba ta dace da al’adun mutanenta ba.

Amma shugaba Moseveni, wanda ya rattaba hannu a kan dokar a watan Mayu, ya ce, “Uganda za ta ci gaba, ko da bashi ko babu.

“Wannan abin takaici ne takaici ne yadda Bankin Duniya da ’yan korensa suke kokarin tilasta mu, mu yi watsi da al’adu da addininmu da kuma ’yancinmu, ta hanyar amfani da kudi.

“Ba ma bukatar kowanne irin matsin lamba daga kowanne mutum wajen magance matsalolinmu,” in ji shi.

Sai dai Shugaban ya ce suna ci gaba da tattaunawa da bankin don ganin ko zai canza shawararsa ya ba su bashin.

A sabuwar dokar da kasar ta Uganda dai ta yi, wadanda aka samu da aikata laifin auren jinsi daya sun aikata babban laifi, kuma za su iya fuskantar hukuncin da ya kai na daurin rai da rai.