Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa aiki ne ya kawo shi kujerar shugaban ƙasa ba wata riba ta azurta kansa ba.
Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samar da sakamako mai kyau da kuma samar da ingantaccen ci gaba a sassa daban-daban da suka hada da ilimi da tattalin arziki mai ɗorewa.
Tinubu wanda ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ƙungiyar tsaffin shugabannin Majalisar Dokokin Tarayya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani, ya jaddada cewa bai hau kujerar mulki ba face sai domin ya yi wa ƙasar nan hidima.
“Ban hau wannan kujerar ba domin neman kuɗi ko don wata riba ba. Na zo na yi aiki. Na nemi kuri’un ‘yan Najeriya kuma suka ba ni,” inji Tinubu.
Kazalika, Tinubu ya jaddada cewar zai ci gaba da jajircewa wajen gabatar wa jama’ar Nijeriya romon dimokuraɗiyya ta hanyar gudanar da manyan ayyuka da samar da abinci da makamashi da tsaro da ilimi tare da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Shugaban wanda ya yaba da goyan bayan da yake samu daga wasu daga cikin tsoffin shugabannin majalisun duk da bambancin jam’iyyar siyasa, ya buƙaci da su ci gaba da sanya ci gaban kasa da kuma haɗin kai a gaba.
Tinubu ya bayyana fatan ganin Nijeriya ta shawo kan ɗimbin matsalolin da take fuskanta, inda ya ƙara da cewar muddin ’yan Nijeriya suka haɗa kansu ba tare da nuna banbanci a tsakaninsu ba, kasar na iya magance ƙalubalen da ake fuskanta kamar yadda wasu ƙasashen duniya suka yi.
Shugaban wanda ya tabbatar da cewa yana sane da halin matsi da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta, ya shaida cewa wasu daga cikin matakan da yake dauka da zummar tinkarar wasu daga cikin wadannan matsaloli tare da janyo hankalin shugabannin da su daina korafe korafe wajen mayar da hankali a kan matakan da ya dace a ɗauka domin gyara.
Yayin jawabinsa, shugaban tawagar, Sanata Ken Nnamani wanda ya bayyana goyan bayansu ga jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ya jinjina masa dangane da matakan da ya ɗauka na ceto ƙananan hukumomi daga kamun kazar kukun da gwamnonin jihohi suka musu.
Sauran waɗanda suka halarci taron akwai tsoffin shugabannin Majalisar Tarayya guda 16 da suka haɗa da tsofaffin shugabannnin Majalisar Dattawa da mataimakansu da kuma takwarorinsu na Majalisar Wakilai.