✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Ban yi zaton samun kyautar N1m a gasar sinadarin Onga ba”

Kamfanin ya gwangwaje kwastomominsa da ke mu'amala da sinadarin ɗanɗano na girki.

Kamfanin Promasidor Najeriya da ke yin sinadarin ɗanɗano na girki, ya bayyana waɗanda suka yi nasara a rukunin farko na Gasar Sinadarin Ɗanɗano na Onga.

Kamfanin ya sanar da waɗanda suka yi nasarar a ranar 13 ga watan Satumba, 2024.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi nasarar lashe kyautar Naira miliyan ɗaya, Amaka Emeh, ta bayyana cewa ba ta yi tsammanin za ta yi nasara a gasar ba.

“Ban taɓa tsammanin zan yi nasarar samun kyautar Naira miliyan ɗaya a wannan lokaci da ake fama da talauci da matsin rayuwa a ƙasar nan ba.”

Shi ma, Abubakar Kabir daga Jihar Neja, wanda ya samu kyautar Naira 500,000 ya bayyana jin daɗinsa tare da yaba wa Onga kan karrama mutanen da suke mu’amula da sinadarinsu ta hanyar yi musu irin wannan karamci.

Wannan na daga cikin ƙoƙarin Onga na saka wa kwastomominsa da wadanda suke yin amfani da sinadari. da kamfanin ke yi wajen girke-girkensu a bikin murnar cikar kamfanin shekara 10 da kafuwa.

Kamfanin zai raba kuɗi da kyaututtuka da na kuɗi hara naira miliyan 250 a yayin gasar.

Taron ya samu wakilcin hukumomin gwamnati da ke kula da shirya gasa irin wannan da raba kyaututtuka.

Hukumomin sun haɗa da Hukumar Kula da Caca ta Ƙasa, Hukumar Gasa da Tabbatar da Gamsuwar Al’umma,da kuma h5ukumar Kula da Caca ta Jihar Legas.

Domin tabbatar da an gudanar da gasar bisa ƙa’ida kuma waɗanda suka yi nasara an bayyana su tare da kuma ba su kyaututtukansu.

A yayin gasar na mai rabo ka ɗauka, mutum 10 sun samu kyautar miliyan ɗaya kowannensu, sai mutum biyar da suka samu kyautar Naira 500,000, mutum 10 sun samu kyautar Naira 100,000.

Har wa yau, mutum 40 sun samu kyautar Naira 50,000, yayin da mutum 325 suka samu kyautar Naira 10,000 sai kuma wasu sama da mutum 300 da suka samu wasu kyaututtuka daban-daban.

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan Promasidor Nigeria, Francois Gillet, ya ce kamfanin ba bikin murnar cika shekara 10 da kafuwa ya yi kaɗai ba.

“Bikin ya haɗa ne da bai wa kwastomomi masu amfani da sanadarinmu na ɗanɗano kyaututtuka domin su shaida cewa tafiyar tare da su ake yi ta hanyar wannan gasa ta ‘Onga taste the Million Promo’.

Adebola Williams, Daraktan Kasuwanci na Promasidor Nigeria, ta ce, “Mun yi farin ciki da wannan kyaututtuka da muke bai wa masu mu’amula da mu. Ina so na sanar da ku cewa yanzu aka fara, akwai wasu shirye-shirye da ke tafe wanda za mu riƙa saka wa masu mu’amula da mu da tarin kyaututtuka masu yawa.

An fara gasar ne a ranar 1 ga watan Satumba, sannan za a ci gaba da yin ta har zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, 2024.

Ga wanda ke son shiga gasar zai sayi jaka ɗaya ta Onga Beef ko Chicken mai dunƙule 90 ko jaka biyu na Onga beef ko jakar Chiken mai dunƙule 50, sai duba ciki domin samun bayanan shiga gasar.

Mutum zai tura lambar da ya samu zuwa 1393 a wayarsa, domin shiga gasar da cin kyaututtuka.

Babban Manajan Kamfanin, Oladapo Oshuntoye, ya ce sun ciri tuta wajen karrama kwastomominsu.

 

Domin samun ƙarin bayani, za a iya bibiyar shafukan Onga na sada zumunta a (IG:@onga_nigeria, FB: @Onga Nigeria, YT: OngaNigeria, TikTok: Onga.Nigeria) ko kuma a shafin yanar gizo:  www.ongamillionspromo.com