✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban yi mamakin fasa taron yakin neman zaben Atiku a Ribas ba —Wike

Ya ce PDP a Ribas ba ta da wadanda za su tara jama'a don gudanar da yakin neman zaben Atiku.

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya ce bai yi mamaki ba dangane da soke taron kamfe da kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP ya shirya gudanarwa a jihar.

Wike, ya ce babu wani da ke da karfin siyasa a jihar da zai iya tara dimbin magoya baya ga PDP domin gudanar da yakin neman zabenta.

Gwamnan na wannan jawabi ne a ranar Litinin a taron jam’iyyar PDP na jihar da aka gudanar a Karamar Hukumar Akuku-Toru, inda ya yi jawabi kan wasu batutuwan siyasa da suka shafi jihar.

Ya bayyana cewa wadanda ke da alhakin shirya yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar ba su da karfin tara magoya baya a Ribas.

Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP daga Kudancin Najeriya sun shiga takun saka da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, kan cewar sai ya yi murabus a matsayin wani sharadi na goyon bayan takarar Atiku a zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tun bayan kammala zaben fid-da-gwanin jam’iyyar, gwamnonin suka kauracewa shiga sabgogin jam’iyyar, inda suke gudanar da tarukansu su kadai.

%d bloggers like this: