Alhaji Ali wanda aka fi sani da Sabon Kida, yana daya daga cikin yaran mawaki marigayi Alhaji Musa dan kwairo. Yanzu yana sana’ar tufkar igiya ne. Aminiya ta gana da shi inda ya yi bayanin yadda ya zama yaron dan kwairo da irin kyaututtukan da Sardauna ya ba su. Ya ce bai taba nadamar zama yaron dan kwairo ba. Ga yadda hirar ta kasance:
Alhaji Ali mai kimanin shekara 80 ya ce ya fara bin dan kwairo ne tun yana yaro, amma ya zama cikakken yaronsa bayan mahaifinsa ya roki dan kwairo hakan, kasancewar dan uwansa ne.
Ya ce idan suna waka jama’a da dama sukan dauka sun yi gaji waka ne, “ya zama kamar mun yi gadon waka ne, ko a ruwa aka ba mu muka sha saboda yadda muke rera wakokinmu cikin tsari.”
Ya ce yana iya tuna irin yadda marigayi Sardauna Sa Ahmadu Bello yake jansu a jiki da nuna musu kauna.
Sabon Kida yana zama a gidansa da ke kauyen Gidan Karo a karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara ne, ya manta abubuwa masu yawa saboda tsufa, duk da haka ya bayyana abubuwa masu yawa da ya iya tunawa dangane da yadda suka gudanar rayuwar wakokinsu, inda ya ce Sarduna ya yi musu kyaututtuka masu yawa da ba za su iya tuna adadinsu ba, hakan ya yi matukar karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da waka.
Ya ce Sardauna ya ba su kyautar motoci da sauran kyaututtukan da ba kowa zai iya samun su ba.
Sabon Kida ya ajiye rigunan da Sardauna ya ba su, inda ya ce za su iya kai shekara 50. Daga nan ya sanya daya daga cikin rigunan da Sardauna ya ba su cikin farin ciki. Duk da kasancewar rigar ta dade amma tana nan da kyawunta da kuma karfinta. Ya ce Sardauna ya ba su kyaututtukan ne a lokacin da suka yi masa waka yayin wani biki na musamman a Kaduna. Ya ce a lokacin bikin an ba su masauki na musamman, an kuma ba su abinci mai kyawu da dadi, sannan aka yi musu ruwan kyaututtuka.
A duk lokacin da zai ambaci Sardauna sai ya ce: ‘Gamji dan kwarai’, don ya nuna irin muhimmanci da yake da shi a rayuwarsa.
A lokacin da ya tuna irin wakoki da kuma rayuwa mai dadi da suka yi a lokacin Jamhuriyya ta farko ne sai ya fashe da kuka. Ya ce bayan mutuwar Sardauna sun dade ba su yi waka ba, saboda jimamin mutuwarsa, daga nan suka ci gaba da waka har suka yi wa Sarkin Musulmi da Sarkin Daura Bashar da Sarkin Zazzau Aminu da sauransu waka.
Ya ci gaba da hawaye bayan an fada masa shi kadai ya rage a ciki yaran dan kwairo, inda ya ce hawayensa na nufin ta’aziyya ga dan kwairo da kuma yaransa.
A yanzu ba shi kadai yake zaune a Shiyau Makada da ke gefen Gidan Kano a kan hanyar Gusau da ke karamar Hukumar Maradun ba. Yana tare da ’ya’yansa 10 da kuma jikokinsa.
Ya ce daidai da rana daya bai taba nadamar kida da wakar da ya yi ba, saboda ya shahara, mutane da yawa na sonsa. Bai kuma taba nadamar zama yaron dan kwairo ba.
Ya ce: “Shekara 26 bayan mutuwar Alhaji Musa dan kwairo, har yanzu akwai wadanda suke wakoki irin nasa, ko a yanzu ma jikan dan kwairo na waka irin ta kakansa.” Inji shi.