✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban taba nadamar nada Sanusi a matsayin sarkin Kano ba – Martanin Kwankwaso ga Ganduje

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce bai taba nadamar nada tsohon Gwamnan CBN Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarkin Kano ba.

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce bai taba nadamar nada tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarkin Kano ba.

Kwankwaso na mayar da martani ne ga kalaman Gwamnan jihar, kuma tsohon mataimakin sa, Abdullahi Umar Ganduje a yayin bikin kaddamar da wani littafi kan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

Ya ce nadin Sanusin a matsayin sarki ya biyo bayan shawarwari da tuntubar masu ruwa da tsaki daban-daban, yana mai cewa kuma an yi shi ne bisa ka’ida.

Kwankwaso ya ce a matsayin san a Gwamnan jihar a wancan lokacin, ya sa irin mutanen da ya kamata ya nemi shawarar su idan zai dauki muhaimman matakai da za su shafi al’umma na tsawon lokaci kamar nadin sarkin da zai gaji marigayi Ado Bayero.

A wurin taron dai Ganduje ya ce ya tube sarkin ne daga sarautar saboda ya ceto gidan sarautar daga lalacewa, yana mai cewa ko a baya ba Sanusin ne ya fi cancanta ya zama sarkin ba.

Sai dai a martanin Kwankwaso ta bakin Babban mai Taimaka Masa kan Al’amuran Cikin Gida, Muhammad Inuwa ya ce ya nada shi ne saboda yana neman wayeyyen sarki da zai dace da zamani.

Ya ce, “Hakika duk wanda ya san Ganduje zai shaida cewa ba mutum ne da ke neman ci gaba ba, hakan ne ma ya sa ko kadan ban nemi shawarar sa ba kafin nada sarkin.

“In banda kasancewar Jonathan a wurin taron, zuwan Ganduje kadai ya isa ya mayar da taron da ya kamata ya zama muhimmi zuwa shiririta

“Ba abin mamaki ba ne ga duk wanda ya san halin Ganduje in ya je irin wannan taron ya rika sharara karya kan abinda ya tabbatar ba gaskiya ba ne kan nadin sarkin har zuwa tube shi da aka yi ba bisa ka’ida ba.

“Na zabi Sanusi ne daga cikin ragowar ’yan takarar saboda ya fi su ilimin addini da na boko.

“Ya fi su gogewa ta aiki. Irin karbuwa da tagomashin da ya samu daga masu zabar sarki da ma al’ummar jihar Kano a wancan lokacin shine ya sa na nada shi.

“Akwai ranar da ba zan manta ba; wata Juma’a 13 ga watan Yunin 2014 inda Gandujen yayin wani shiri da aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na Channels da rediyo Freedom yake cewa Sanusin ne ya fi cancanta a tsakanin dukkan ’yan takarar sarkin.

“Saboda haka, ya je ya hau mumbari ya rika daba wa cikin sa wuka saboda tsabar son zuciya ya ma wuce munafunci.

“Muna sane da cewa Ganduje ya cire Sanusi ne saboda ya wargaza tarihi da sarautar Kano. Kowa ya san Sanusi mutum ne mai son ci gaban Kano ta kowacce fuska, wannan ne kawai dalilin da ya sa halin su bai zo daya ba.