✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban taba karbar albashi ba tun da na hau mulki — Soludo

Da gangan na fito da wasu tsare-tsare don rage kashe kuɗi daga asusun gwamnatin jihar.

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce ya shafe shekara biyu cif ba tare da ya taba karbar albashi ba, tun bayan da ya zama gwamnan jihar.

Soludo ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Akwa, babban birnin jihar, yayin bikin cikarsa shekara biyu da hawa mulki.

Soludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya na CBN ne, ya kuma karyata rade-radin cewar matarsa na da mota a hukumance.

“A yanzu haka da na ke magana da ku, ba na karɓar albashi, gwamnatin Jihar Anambra ba ta biya na albashi ba.

“Kuma mai ɗakina ba ta da wata mota a hukumance, har yanzu motocina ta ke tukawa,” in ji Soludo.

A cewar gwamnan, da gangan ya dinga aiwatar da wasu ayyuka domin toshe hanyoyin zurarewar kuɗi daga asusun gwamnatin jihar.

Ya ce: “Duk wani gwamna da ya zo yana zuwa da tsarin karɓo bashi da sauransu, amma mun yanke shawarar zuwa da wani sabon salo a waɗannan shekaru biyu da suka gabata.

“An sha tambaya ta; ta yaya kuke tafiyar da gwamnati ba tare da karɓo bashi ba? Amsata a ko da yaushe ita ce, muna yin hakan don kawo sabon sauyi a tsarin tafiyar da gwamnati.”