Alhaji Dokta Shehu, ya ce shi ne Sarkin Mayun Najeriya a tattaunawarsa da Aminiya Sarkin Mayun wanda ke zaune Lafiya a Jihar Nasarawa ya bayyana dalilan da suka sa ake kiransa da Sarkin Mayu da yadda jama’a ke kallonsa da sauran batutuwa da suka shafi harkar:
Za mu so ka bayyana taKaitaccen tarihinka?
Ni mutumin garin Akurba ne da ke cikin garin Lafiyar Barebare fadar Jihar Nasarawa. Na yi karatuna a nan tun daga firamare da sakandare har zuwa babbar makaranta. Har yanzu ina ci gaba da karatu.
- Jikan Sardauna, Magajin Garin Sakkwato, ya rasu
- Rikicin Ukraine: Rasha ta fara gwajin manyan makamai
Me ya sa ake kiranka da Sarkin Mayu?
Ana kirana da Sarkin Mayu saboda wasu dalilai. Amma asali na gada ne iyaye da kakanni. Mun gaji abin ne a gidanmu. Allah Ya ba mu baiwar magungunan abin da ya shafi maganin mayu da aljanu.
To sanadiyyar haka ake kirana Sarkin Mayu. Domin duk mayen da aka kawo shi nan gabanmu to da izinin Allah zai mika kai. Hakan ya sa na samu lambar yabo daban-daban, har ta kai ake kirana Sarkin Mayu.
Kuma ni ne Shugaban Majalisar Sarakunan Mayu na Afirka.
Mutane sukan dauki maita a matsayin tsafi, shin ita maitar iri-iri ce?
Eh, ita maita iri-iri ce. Akwai maitar da baiwa ce da Allah ke sa a haifi mutum da ita, wani kuma yakan sha a nonon mahaifiya ne wani da kansa yake nemanta, wani kuma yana nema da niyyar kariya amma sai ya rika cutar da jama’a da ita. Saboda haka ne ire-iren wadannan mutane muke maganinsu.
Don maye idan ya ganka, ya san abin da ka ci ko ka sha, saboda hakan idan ba karfin addu’a ba, sai ya yi kokari ya kama taurarin mutum, shi bai yi amfani da su ba, kuma bai bari ka amfani al’umma ba.
To gaskiya irin wannan maita tsafi ce, sabon Ubangiji ne kuma shirka ce.
Shin wane irin kallo jama’a suke yi maka a lokacin da aka yi maka sarautar Sarkin Mayu?
Gaskiya ba abu ne mai sauki ba. Tun daga nan na fara taka matakai da dama, don wadansu gani suke yi ba zan yi tsawon rai ba. Wadansu na cewa abar ni, karar kwana ce ta kai ni, amma cikin ikon Allah ga shi har yau muna ta fama kuma muna taimaka wa jama’a. Karshe har ta kai ni ne Sarkin Mayun Najeriya da Afirka a yanzu ba inda ba a san ni ba.
A matsayinka na Sarkin Mayu, Me ye ainihin aikinka?
Aikina shi ne ina yin harka ta gargajiya don gado na yi. Haka umarni ne na iyaye duk da na yi karatu. Akwai lalurar da za ka ga idan aka yi wa mutum allura sai kawai ya suma, akwai wanda idan aka kawo shi, sai ka ga an kawo shi ranga-ranga saboda ciwon yana ta karuwa, wani ma za ka an kai shi asibiti, an yi maganin, an yi maganin amma babu sauki, amma da an kawo shi nan sai ka ga ya samu sauki.
Bayan haka ina sana’ar kiwo da harkar gidaje da kamfanoni, amma abin da na fi damuwa da shi, shi ne na taimaka wa mutane ta hanyar kiwon lafiya.
To idan aikinka ya shafi maita, shin ka taba haduwa da wani ko wata mayya da suka wahalar da kai a aikin?
To, amma cikin ikon Allah, Ubangiji Yana taimakonmu a kansu. Muna da mabiya da yawa, ta shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da sauransu da suke taimaka mana da addu’a.
Ban taba arangama da mayen da bai taba mika wuya ba, wani idan ya sa ranar da zai zo wurina sai ka ga ya samu lafiya, wani yana shigowa garin Lafiya sai ka ya samu lafiya, wani ma yana shigowa kofata ko dakina sai ka ga ya samu lafiya. Gaskiya Allah Ya hore mini mayu da aljanu, suna ba ni hadin kai sosai.
Akwai bukukuwan mayu da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta, shin yaushe za a gudanar da waDannan bukukuwa?
Eh, gaskiya ne akwai zaman da nake yi a matsayina na Sarkin Mayu inda nake gayyatar mayu daga Najeriya da sauran kasashe da dama kamar su Ghana da Kwaddibuwa da Nijar da Masar da sauransu.
Yanzu muna so mu gudanar da babban biki wanda za mu gayyaci Sarkin Musulmi, ya zo ya gani, yadda za mu tona asirin mayu, mu kunce kurwar mutane kowa ya gani.
Sannan a cikin wannan shekara ta 2022, akwai wani abu da mayu ke yi wanda muka gano suna cutar da al’umma, inda mayun suke kama kurwar matasa da suke karatun boko ko neman aiki, sai su kama su su shanye jininsu, a binciken da na yi na gano cewa miyagun, sun yi zama inda dodonsu ya ce yana son jarirai ne, inda za su yi amfani da wurare biyu, asibiti da gidajen ungozomomi, kuma jaririn da suke so su ne sababin haihuwa wadanda ba su yi awa biyu ba.
Sannan idan mace ta haihu sai su sa wani abu kamar allura suna janye jininta, duk maganin da za a yi ba zai tsaya ba sai an yi addu’a sosai. Muna ta shirye-shirye kuma nan ba da jimawa ba za mu sanya ranar bikin kuma za mu sanar da jama’a.