Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce bai taɓa tsammanin zai kai shekara guda a matsayin gwamnan jihar ba, biyo bayan rikicin siyasa da ya faru tsakaninsa da uban gidansa, Nyesom Wike.
An rantsar da Fubara a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sai dai ba jimawa da hawansa mulki rikicin siyasa ya ɓarke lamarin da ya kai majalisar dokokin jihar fara shirye-shiryen tsige shi.
- Likitocin Kano sun fice daga yankin aikin NLC —NMA
- NLC ta kashe wuta daga babbar cibiyar lantarkin Najeriya
Da yake jawabi yayin bikin cikarsa shekara ɗaya a kan mulki a ranar Lahadi, Fubara ya ce, “Wasu watanni da suka wuce, babu wanda zai yi tsammanin cewa za mu kawo yanzu, Ubangiji, na gode da ka ba ni wannan dama, har muka kawo wannan lokacin.”
Gwamna Fubara, ya ce yana sane da irin yadda aka yi ƙoƙarin kawo wa gwamnatinsa cikas.
Ya ce, “Ba za ku gane ba. Zan iya faɗa muku cewa tun kafin mu fara wannan tafiya, akwai shirin kawo mana cikas. Amma cikin ikon Ubangiji ba su yi nasara ba.
“Yanzu, idan muna da Ubangiji a tare da mu ba na tunanin muna da wata matsala. Ina so na gode wa duk wanda ya zo nan don taya mu murna.”
Gwamna Fubara ya yi alƙawarin ba zai ci amanar jama’ar suka aminta da shi ba, inda ya ce zai ci gaba da aiki don kyautata rayuwar al’ummar jihar.
Ya ce, “Abin da shaiɗan ya yi nufin aikatawa shi ne mugunta, amma Ubangiji Ya mayar da shi alheri a gare mu.
“Ba zan bai wa kowa wannan rana ba, ba zan yi magana a kan kowa ba, zan ce kawai, ‘Ubangiji na gode’.”