✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban koma jam’iyyar PDP ba, Inji Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ke wakiltar Kano ta Tsakiya ya karyata rahoton cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP. Aminiya…

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ke wakiltar Kano ta Tsakiya ya karyata rahoton cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Aminiya ta ruwaito jiya cewa labarai a Yanar Gizo sun nuna cewa Kwankwaso tare da ’Yan Majlisar Wakilai 10 daga Jihar Kano sun bar jam’iyyar APC zuwa PDP.
Kwankwaso ya yi watsi da rahoton ne ta hannun Mai Taimaka Masa, Nafi’u Umar Dankura inda ya ce yana nan a jam’iyyar APC.
“Ina so na karyata labarin karya da jita-jitar da wasu kafafen yada labarai na Yanar Gizo da wasu gidajen rediyo suke yadawa cewa wai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP. Wannan ba gaskiya ba ne. Kamar yadda kowa ya sani Kwankwaso ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafa jam’iyyar APC saboda haka har yanzu yana daya daga ciki ginshikan jam’iyyar”. Inji Dankura.
Ya bayyana cewa Kwankwaso wanda yake jagorancin Kwamitin Tsare-tsare na Kasa ba shi da niyyar barin jam’iyyar APC.