Paris Saint-Germain ta ki amincewa ta sayar da dan wasan gabanta, Kylian Mbappe, ga Real Madrid a lokacin cinikayyar ’yan wasa duk da cewa dan wasan ya nuna sha’awarsa na barin kungiyar.
Amma Mbappe ya hakura tare da ci gaba da zama a PSG duk da cewa burinsa na barin ta bai cika ba, kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da RMC Sport.
- Gawurtattun ’yan bindiga da aka cafke a Zamfara
- Masu garkuwa da Babban Sakatare a Neja na neman N60m
“Na sanar da su cewa ina son tafiya, shi ya sa na ki sabunta kwantaragina.
“Na so a ce kungiyar ta samu wasu kudade a cinikayyar da za ta iya amfani da su ta sayi wanda zai maye gurbina.
“Tun tuni na sanar da su cewa ina son tafiya, amma suka ki yin komai a kai. Duk da haka ina fatan dukkaninmu za mu amfana a gaba.
“Gaskiya ban yarda cewa sai ranar karshe ta cinikayyar ’yan wasa ba sannan za a ce za kammala komai.
“Ina nan a kan bakata, na bayyana ra’ayina tun tuni kuma na fada a kan lokaci.
“Amma zan girmama shugabannin wannan kungiya idan ba su so na tafi zan zauna,” a cewar Mbappe.