Tsohon Sakataren Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Musa Amadu ya karyata rahoton da ke cewa ya janye daga takarar neman shugabancin kungiyar na kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, Amadu na daga cikin ‘yan takara 11 da ke neman shugabancin na NFF a zaben da za a gudanar ranar Juma’a a Benin, babban birnin jihar Edo.
- Yarjejeniyar zaman lafiya: Ba a ga Tinubu ba a wajen rattaba hannun ’yan takara
- 2023: Na rungumi kaddara kan hukuncin kotu na hana ni takara – Ahmed Lawan
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, Amadu ya bayyana rahoton ficewarsa daga takarar a matsayin na kanzon kurege.
Tsohon Sakataren na NFF din ya bai wa magoya bayansa tabbacin da shi za a yi zabe, don haka kada su ji wani tsoro.
“Da ni Musa Amadu za a yi zaben ranar 30 ga Satumba, a Edo,” inji shi.
A baya, wata Babbar Kotun Abuja ta ba da umarnin dakatar da zaben na NFF biyo bayan karar da wasu suka shigar na neman a yi adalci a tafiyar da ita.
(NAN)