✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban gamsu da ’yan majalisar yanzu ba -Sarkinbai Kano

Alhaji Mukhtar Adnan, Sarkinbai Kano, Hakimin dambatta a Jihar Kano,  a jiya Alhamis ne ya  cika shekara sittin a kan karagar mulki. Shi ne sarkin…

Alhaji Mukhtar Adnan, Sarkinbai Kano, Hakimin dambatta a Jihar Kano,  a jiya Alhamis ne ya  cika shekara sittin a kan karagar mulki. Shi ne sarkin gargajiya da ya fi dadewa a kan karagar mulki a jihohin Arewa a yau, kuma yana daya daga cikin ’yan majalisar zabe da nadin sarki su hudu da suka nada Sarkin Kano a shekarar 1962. Aminiya ta samu tattaunawa da shi, inda ya yi tsokaci kan rayuwarsa da al’amuran da suka shafi siyasa a zamanin da da na yanzu, kamar haka:

Ko za ka ba mu takaitaccen tarihinka?
Godiya ta tabbata ga Allah, Madaukakin Sarkin da Ya raya ni zuwa yanzu. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad. Akwai wadanda muka tashi tare, yanzu ba su. Allah Ya karbi ransu, saboda haka ina gode maSa da Ya raya ni, har yau ga shi ina bikin cika shekara sittin [a kan wannan sarauta]. Bayan haka ina godiya ga mahaifina Muhammadu Adnan da mahaifiyata Hajiya Maimunatu, [saboda] irin tarbiyyar da suka yi min zuwa yanzu, Allah Ya jikansu kuma Ya gafarta musu.
To ni dai an haife ni a nan cikin garin dambatta a kofar Gabas, inda mahaifina yake, inda ya yi malanta. Bayan na kai shekara hudu, ya sa ni a makarantar kur’ani har lokacin shigata firamare, wadda ake cewa elmantare daga 1935-39; sai kuma na shiga Middle School, wadda ake kira Rumfa College yanzu, daga 1939 zuwa1944.
To bayan na gama, sai mahaifina ya sa ni na yi aikin Malamin Hakimi a Ringim na shekara guda, daga nan sai na dawo dambatta, kafin lokacin da ake neman a dauki yara aiki aka tura ni Zaria Clerical Training College (CTC), inda na shekara guda. Saboda kwazona aka kai ni Kaduna Northern Region na zama Odita, sannan aka dawo da ni Bompai Kano, a shekara ta biyu. Da na gama, sai na koma N.A. ta Kano, aka kai ni baitulmali (wato Treasury) har lokacin da siyasa ta zo.
Ba zan manta da wannan shekara ba 1954, a wannan shekara ne aka nada ni Hakimin dambatta, Sarkinbai. Yau shekara sittin daidai. Bayan haka, a wannan shekara ne aka zabe ni dan majalisar tarraya da ke Lagos, nake wakiltar mazabar kiru da karaye.
Daga nan fa abubuwa suka yi ta tafiya. A can Lagos na dage na yi aiki da kwazo har ya sa suka gane ni suka nada ni a matsayin Chief Whip, matsayin da na rike har sanda aka yi juyin mulki na 1966.
To ya zaman Lagos ya kasance a wancan lokaci, ganin ka saba zama a dambatta?
E, haka ne, ka san lokacin ba zama dindindin ba ne, za a je duk sanda majalisa za ta zauna sati daya, kwana goma ko wata daya, sannan na dawo, haka na rika yi.
To lokacin da aka yi juyin mulki muna House, ranar Asabar 16 ga Janairu da safe na fito na shiga majalisa, sai na ga sojoji kewaye da majalisa, na ce me ke faruwa, sai aka ce an yi juyin mulki ne. To Speaker ya zauna, mu ma muka zauna, sai wani I.B.K. Okafor ya ce yana kiran a janye zaman majalisar domin abin da ya faru. Kuma haka aka yi har mulkin soja ya kankama.
To ka dawo dambatta ke nan?
E, na dawo na ci gaba da aikin Hakimi. Sai aka ce domin a zauna lafiya ’yan majalisa na da a ba su aiki, sai marigayi Gwamnan Kano Audu Bako (Allah Ya jikansa) ya nada ni Kwamishinan Ilimi, inda na yi shekara bakwai ina aiki. Mun yi aiki sosai domin mun kara yawan makarantu kuma mun debi malamai aiki.
Ya kake ganin tabarbarewan ilimi tun daga wancan lokaci zuwa yanzu?
E, abubuwa sun kara lalacewa, saboda  mun kara yawa, domin an ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai. An ce kowa sai ya yi ilimi, amma makarantun kadan ne. Dalilin da ya sa aka kirkiro abin da ake kira ‘crash programme’ ke nan, sannan ba malamai. Audu Bako ya ce mu je Kudu, kamar Enugu da Ibadan mu debo malamai, kuma haka muka yi. Shi ya sa aka yi ta surutu wai mun je mun debo wani jinsi, amma duk da haka, Alhamdulillahi, zamansu ya sa harkar ilimi ta bunkasa.
To bayan an shiga siyasar jamhuriya ta biyu fa?
Babu wani abin da na tabuka a siyasa na wannan lokaci domin ina nan tare da Mai Martaba ina aikina na Hakimi.
Yaya cigaban masarautarka tun da ka zama Hakimi a dambatta?
Gaskiya an samu cigaba ta kowanne fanni, domin baya daga birnin Kano, babu wata masarautar da ta kai dambatta yawan mutane da ke da ilimi a Jihar Kano. Wannan ya samu ne saboda ilmantar da muka yi ta yi wa iyaye su sa ’ya’yansu a makaranta. Shi ya sa daga ma’aikatun karamar hukuma zuwa jiha da gwamnatin tarayya, babu karamar hukumar da ta kai dambatta yawan ’yan boko.
Sai bangaren zaman lafiya. Muna zama lafiya a dambatta, mu abin da muka gada daga wajen kakanninmu shi ne noma, saboda haka harkar noma ta bunkasa.
Wajen fannin ayyuka fa an ce akwai aikin gidan talabijin na kasa da har yanzu ba a gama ba?
Shi wannan NTA, mun sha magana. Mun je wajen gwamna da sauran manyan ma’aikatan gwamnati, sun ce akwai wani dalili a Abuja da ya rike wannan aiki, amma kwanan nan za a kammala, inshaAllah.
To bangaren kiwon lafiya fa?
Babban jin dadina shi ne wannan babban asibiti na dambatta, marigayi Sardauna Ahmadu Bello shi ne ya gina shi tare da mutanen Jamus kuma yanzu wannan asibiti ya kasaita kuma musamman Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya taso haikan wajen kara bunkasa wannan asibiti, musamman wajen magunguna da wajen kwanciya.
Ka yi zaman majalisa tun jamhuriya ta farko, yaya kake ganin zaman majalisa ta yanzu, akwai wasu gyara da za su iya yi?
Ni dai na gode Allah zaman da na yi na shekara goma sha biyu a majalisar tarayya har na samu mukami, na gode Allah. Na sha gwgwarmaya da manyan mutane domin ni ne kakakin jama’ar Arewa a Lagos. Kamar lokacin da Cif Awolowo ya yi wata tafiya zuwa Ingila ya la’anci gwamnatin Tafawa balewa ni aka sa na yi ‘motion’ na la’ance shi, da kuma irin su Jaja Wachukwu mun je majalisar dinkin duniya tare, duk ba zan manta wannan ba. Kuma akwai mutane irin su marigayi Malam Aminu Kano, mun yi aiki duk da dai yana NEPU ni ina NPC.
Wato ka gamsu da yanda ’yan majilisar yanzu suke tafiyar da aikinsu?
Ina! Ai ban gamsu ba ko kadan, domin ban yarda cewa aikin majalisa ya wuce ka ce wai sai an ba ka kudi za ka yi aiki ba,  ko daya, kuma ban goyi bayan wannan albashi da ake ba su ba, ya yi yawa.
To yawan canza sheka da suke yi kuma fa a yanzu?
In an canza sheka, da yake zamani ya canza, babu laifi, watakila wannan zamani ne ba irin namu ba, sai dai mu sa ido mu yi musu addu’a Allah Ya kawo zaman lafiya.
Wane kira za ka yi ga jama’ar masarautarka?
Kiran da zan yi shi ne a ji tsoron Allah kuma a hada kai kuma a yi wa jama’a aiki, ko dan majalisa ne ko karamar hukuma ko na tarayya ne a hada kai a yi wa jama’a aiki, a daina hayaniya domin kasa ta cigaba.