✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban ce duk lalacewar Kirista ya fi Musulmi cancanta ya shugabanci majalisa ba – Shettima

Ya ce sam ba haka yake nufi ba, juya masa magana aka yi

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya nesanta kansa da wasu kalamai da ya ce ana alakanta shi da su kan shugabancin Majalisar Dattijai.

Aminiya ta rawaito cewa wani faifan bidiyo ya yi ta karade gari musamman a kafafen sada zumunta, inda aka hango Shettima a wajen wani taro da Sanatoci ranar Lahadi cewa “gwara Kiristan Kudu duk lalacewarsa da Musulmin Arewa duk nagartarsa ya Shugabanci Majalisar Dattawa.”

Kalaman nasa dai sun jawo cece-kuce matuka, musamman a shafukan sada zumunta na zamani a ranar Litinin.

Shettima, a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Kasa ya fitar da yammacin Litinin ya ce an canza masa kalaman nasa gaba daya, kuma an yi masa mummunar fahimta.

Ya ce ba a bayyana kalaman a muhallin da aka yi su ba, kuma an canza musu ma’ana don kawai su dace da manufar masu zagon kasa ga burin al’ummar Najeriya na tabbatar da hadin kan kasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a yayin taron da ’yan Majalisar Dattijai masu gangamin ganin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin sun jagoranci Majalisar Dattijai ta goma, Kashim Shettima ya jaddada tsarin siyasar kasar inda ya yi nuni da cewa samun Kirista daga Kudancin Najeriya da kuma wani Musulmi daga Arewaci shi ne zai tabbatar da daidaiton adalci don inganta muradin shigar da kowa a dama da shi a gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ambato Sanata Shettima yana nunar da cewa, bisa la’akari da cewa Shugaban Najeriya da Mataimakinsa duk Musulmai ne, to bai dace su goyi bayan Musulmi ba, ko da kuwa Musulmin da ya fi cancanta, saboda tabbatar da daidaito.