Dan Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu na farko mai suna Emeka Ojukwu Karami ya yi Alla-wadai da rahotannin da aka yada a kafafen sadarwa cewa ya karyata maganar da Shugaba Buhari ya yi kan tattaunawar ya ce ya yi da mahaifinsa.
Ya ce bai gana da wata kafar yada labarai ba ko kuma tura wani sako ta yanar gizo da ya nuna ya karyata ganawar da Buhari ya yi da mahifinsa.
A sanarwar da ya fitar jiya a garin Awka, Ojukwu Karami ya ce tabbas mahaifinsa ya gana da Buhari kafin mutuwarsa.
Ya kara da cewa duk abin da Shugaba Buhari ya fada a jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya ta kafafen yada labarai gaskiya ne.
“Da farko dai zan ce ban yi maganar da wani ba kuma na biyu shi ne na san cewa duk maganar da Buhari ya yi gaskiya ne. Amma kawai sai na gano wasu na yada kalaman karya suna jingina su gare ni a kafofin yanar gizo. Ban san wandanda suka kintsa wannan lamari ba kuma ban san manufarsu ba” Inji sanarwar.