✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bambanci Tsakanin Nau’ukan Mai

Kamar yadda aka lura a ‘yan makonnin da suka shude, an yi bayani akan nau’ukan suga da gishiri da yadda suke iya shafar lafiyarmu. Inda…

Kamar yadda aka lura a ‘yan makonnin da suka shude, an yi bayani akan nau’ukan suga da gishiri da yadda suke iya shafar lafiyarmu. Inda aka ga cewa suga na da alaka da ciwon suga, gishiri kuma na da alaka ta kut-da-kut da hawan jini. A yau kuma za a duba nau’ukan mai da mukan ci a abinci yau-da-kullum, wadanda su kuma ke da alaka da ciwon kiba.

Mayukan da mukan ci su ma nau’i nau’i ne, domin akwai mai na tsirrai, akwai na dabbobi, akwai kuma dan kamfani wanda aka kirkira. Mayukan tsirrai misalansu sune; man gyada, man ja, man kwakwa, man kade ko kadanya, man zaitun, man waken soya, man ridi da sauransu. Na dabbobi misalansu sun hada da man shanu, kakide, man kifi, man bota da sauransu. Sai kuma na wadanda aka kirkira a kamfani wadanda sabbin zuwa ne, kuma ba su fara zuwa kasuwanninmu ba ma, wasu kuma ana nan ana kera su. Ba za a iya cewa kacokan mutum ya daina amfani da mai ba, domin akwai sinadaran maiko da jiki ke bukata yau-da-kullum wadanda kuma jiki ba ya iya yin su, dole a man abinci ake samunsu.

Mayukan tsirrai suna da amfani sosai ga lafiyarmu. Sai dai akwai wadanda suka fi wasu lafiya. Wadanda suka fi amfani ga jiki sune a kimiyyance ba su da daskararren kitse (abinda ake kira ‘unsaturated fat’) da sinadarin cholesterol sosai, wadanda magudanan jini, da zuciya suka fi so. Su kuma masu daskararren kitse wato ‘saturated fat’ da sinadarin cholesterol, su ne jiki bai cika sonsu da yawa sosai ba, saboda sukan makale a magudanan jini da zuciya. Yadda za a gane mai na da daskararren kitse sosai shi ne idan aka ajiye shi a wuri mai dan ni’ima ba mai sanyi ba, kuma ba mai zafi ba, daskarewa zai yi, akasin mai maras daskararren kitse wanda ko ya dade a ajiye ba ya daskarewa. Misalan man tsirrai da ke da daskararren kitse su ne man ja da man kwakwa. Su kuma misalan mai mafiya karancin wannan kitse su ne irinsu man zaitun da man canola. Daga su sai man fiya, sai a yo sama kan matsakaita kamar man gyada wanda muka fi amfani da shi.

Mayukan dabbobi ma suna da amfani ga jiki sosai. Su ma akwai wadanda jiki ke so, akwai kuma wadanda jiki bai cika son su ba da yawa. Wato su ma akwai masu daskararren kitse sosai a cikinsu, akwai kuma marasa daskararren kitse. Masu daskararren kitse su ne kamar man shanu da man bota da kakide. Marasa yawan daskakararren mai sune kamar man kifi, wanda zuciya da kwakwalwa suke so sosai. Su ma za a iya bambance su ta bangaren daskarewa idan aka ajiye su na wani lokaci.

Wani amfani da mayukan dabbobi suka fi na tsirrai shi ne cewa ana iya samun sinadarin bitaman na rukunin A da na D, wadanda ba a samu a cikin na tsirrai. Sa’annan kuma su mayukan dabbobi sukan dade a wuta wajen suya kafin su kone, don haka za a iya amfani da su sau da dama basu lalace ba, akasin mayukan tsirrai, wadanda sukan iya konewa su lalace bayan suya daya ko biyu dangane da zafin wutar da suka ji. Idan suka kone din kuma sukan samar da wasu sinadarai da jiki ba ya so. Wato kenan komi kyawun man tsirrai idan aka dade ana amfani da shi lalacewa yake. Wasu sukan ce idan an yi suya sau kamar uku zuwa biyar sai a hakura da shi. Kai ko da bai dade ba, idan ana bulbula masa wuta wajen suya zai iya lalacewa ya samar da sinadarai masu guba. Don haka ne ake so a rika amfani da mayukan tsirrai na dan lokaci, musamman na suya, a kuma daina bulbula musu wuta suna kauri suna konewa.

Sai nau’in mai na karshe wanda muka yi bayanin cewa akwai sabon mai kirkirarre da aka fara amfani da shi a kasashen da suka ci gaba. Shi wannan mai an yi shi ne na musamman ba daskararren kitse ko kadan, kuma ba ya kara wa jiki komai, kamar dai yadda akan samu wasu nau’ukan sukari wadanda ba sa kara wa jiki komai, masu abin da ake kira ‘zero calory’, ganin irin yadda mai ke sa jama’a mummunar kiba. Don haka ana ganin nan gaba kadan idan bincike ya yi nisa kasuwarsa za ta habaka, ma’aikatan lafiya kuma za su iya ba da shawarar amfani da shi irin wannan mai domin kiyaye kiba ko rage ta.

To a wannan gaba idan za a yi tambaya a iya cewa to duk a jerin ire-iren mayukan nan wanne ne ya kamata a rika amfani da shi? Babu amsa guda daya tak domin saisaitawa ake. Ba za a ce mutum ya dogara kacokan a man girki nau’i daya ba, domin kowane irin mutum da irin bukatunsa na cimaka. Misali mace da namiji na da bambancin bukatu ta bangaren amfani da mai da kitse, haka a tsakanin manya da yara akwai irin wannan bambanci. Mata sun fi bukatar mayuka masu daskararren kitse domin akwai sinadarai da dama wadanda dole sai ana cin kitse za a sarrafa su. Wato jikin su matan ya fi na maza iya sarrafa kitse. Wani aiki ne daga cikin ayyukan sinadarin estrogen, ya rarraba kitse a jikin mace inda suka dace, ya kuma ba da umarnin sarrafa wasu sinadaran a jiki, ya kuma hana maiko ya taru a magudanan jini da zuciya. Amma hakan ba yana nufin mata su rika cika mai ko kitse a abinci ba, a’a komai a yi shi daidai gwargwado a kimance, musamman ma a wadanda suke cikin hadarin kamuwa da mummunar kiba. Haka ma yara, dole ne a rika ba su mayuka masu sinadaran bitaman tunda mun zayyana wadanda suke da bitaman saboda su kuma sun fi mu bukatar sinadaran bitaman.

 

Da ina gani dishi-dishi, da na je asibiti aka auna hawan jini aka ga ya hau. Sai aka dora ni a magani na fara shan rabi, sai gani dishi-dishin ya tafi. To amma yanzu ya dawo. Shi ne nake neman shawara.

Daga Mustapha Habeeb, Kano

 

Amsa: To ko ka tsayar da maganin ne ya sa gani dishi-dishin ya dawo? Watakila baka san cewa hawan jini na iya kashe idanu ba. Shawara a nan ita ce, shi likitan da ya dora ka a kan magungunan ka koma ka masa bayani. Na tabbata idan ka masa irin wannan bayani zai turaka bangaren ido a bincika ko hawan jinin ya fara taba ido. 

 

Ni ma dai ciwon idon ne ke damuna, sai ya yi ja, wani zubi kuma shudi. Ko haka matsala ce?

Daga Maryam Y.

 

Amsa: kwarai za ta iya yiwuwa matsala ce. Don haka ke ma ba ki ga ta zama ba, sai kin ga likitan ido.