✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bambanci tsakanin kayyade iyali ko tazarar haihuwa (2)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku a kan hanyoyin kayyade iyali da tazarar…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku a kan hanyoyin kayyade iyali da tazarar haihuwa. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da su, amin.
Tazarar Haihuwa: Na nufin yin amfani da wasu hanyoyi don hana haduwar kwayayen haihuwar mace da na namiji, amma na wucin gadi ba na dindindin ba, don samar da tazara tsakanin wannan haihuwa zuwa ta gaba.
Hukuncin Tazarar Haihuwa:

Ya zo a wani ingantaccen Hadisi, inda Jabir, Sahabin Manzon Allah SAW, ya ce:
“Mun kasance muna yin azlu lokacin Manzon Allah (SAW) yana cikinmu kuma ana kan saukar da wahayi na Alkur’ani Mai Girma.”
Abin fahimta daga wannan Hadisi mai daraja shi ne, yin azlu, ko wani abu makamancinsa don hana daukar ciki na wucin gadi, ya halatta. Domin in da bai halatta ba da Manzon Allah (SAW) ya hana sahabbansa aikata haka, ko kuma da an saukar da wata aya da za ta haramta aikata shi.
Wannan dalili ne ya halatta yin amfani da hanyoyin hana haihuwa na wucin gadi ga ma’aurata, matukar suna da kwakkwarar hujja ta yin haka din, kamar don kauce wa aukuwar ciki da goyo a lokaci daya, ko don tsoron lafiyar uwa ko da, da sauran makamantan dalilai; amma ba da nufin gudun haihuwa ko kyamar tara ’ya’ya da yawa ba. Kamar yadda ya zo a satin da ya gabata, bai halatta Musulmi ya ‘kyamaci tara ’ya’ya da yawa don ra’ayin kansa kawai ba, domin Allah da ManzonSa duk sun yi hani ga aikata hakan.
Dalilan da ke halatta tazarar haihuwa:
1.    Don kare lafiyar uwa da da: dawainiyar daukar ciki da haihuwa na jigata wasu matan, har hakan ya kai ga raunata lafiyarsu. A irin wannan yanayi idan wani cikin ya kara bullowa zai zama babbar barazana ga rayuwarsu da kuma lafiyar dan da ake goyo da kuma lafiyar sabon cikin da ke tsirowa; ko kuma in ya kasance matar tana da wani ciwo mai tsanani, wanda bullowar ciki na iya zama barazana ga rayuwarta, kamar mace mai ciwon sikila, asma, ciwon zuciya da makamantansu, ko mai wata cuta, wacce aka iya gadar da ita ga abin da za a haifa; to a nan ya halatta a tsaida haihuwa na tsawon lokacin da zai isa har matar ta samu lafiya da karfin da za ta iya jure daukar wani cikin da shayar da shi.
2.    Don mahaifa ta huta: Idan ya tabbata mace mai yawan daukar ciki ce akai akai, wato mai yin ciki da goyo; to ya halatta a dakatar da haihuwa na wani lokaci, don mahaifa ta huta kuma ta koma daidai ta yadda za ta samu karfin daukar wani sabon cikin ba tare da matsala ba. Domin takura mahaifa irin haka na iya haifar da matsala ga lafiyar mai cikin ko a samu wata tangarda yayin daukar cikin da haihuwa.
3.    Don cika lokacin raino: Kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani Mai Girma, tsawon lokacin shayar da yaro shi ne wata 24; don haka kowane jariri yana bukatar wannan tsawon lokacin yana shan nonon mahaifiyarsa; wanda bullowar wani sabon ciki na iya sa a katse yaro daga shayarwa ba tare da ya cika lokacin shayarwarsa ba. Don haka ya halatta a dakatar da haihuwa na wucin gadi don tabbatar da cewa jariri ya cika lokacin shayarwarsa.
4.    Kasawa ga tarbiyya: Haka ma ya halatta a yi tazarar haihuwa don a guji kasawa wajen ba ’ya’ya kyakkyawar tarbiyya idan an tara su da yawa, domin rashin ba su kyakkyawar tarbiyya babbar illa ce ga rayuwar duniyarsu da lahirarsu da kuma barazana ce ga ci gaban al’umma.

Ko ya halatta yin tazarar haihuwa don tsoron talauci?
Wani dalilin da ke sa wasu yin tazarar haihuwa shi ne don gudun nauyin da zai karu wajen kula da ’ya’yan idan sun yi yawa. In muka yi la’akari da bayanin Ayoyin Alkur’ani Mai Girma, inda Allah Madaukakin Sarki ke cewa:
 “Kuma kada ku kashe diyanku domin talauci, mu ne muke azurta ku, ku da su.” k:6:151
“Kuma kada ku kashe ’ya’yanku domin tsoron talauci; Mu ne ke azurtasu, su da ku. Lallai ne kashe su ya zama kuskure babba.” 17: 31.
Allah Ya fada karara cewa Shi ke bayar da arziki ga iyaye da kuma diyan da za su haifa, don haka abin da ya fi dacewa ga Musulmin kirki shi ne ya yi imani  kuma ya kyautata zato ga Allah cewa duk yawan ’ya’yan da Allah Ya ba shi, to kuwa Zai hore masa abin kula da su. Duk wani rai da Allah Ya halitta, to Ya tanadar masa iyakar arzikinsa har zuwa ranar da rayuwar za ta kare.
Haka kuma, Abu Sa’id AlKhudriy, Sahabin Manzon Allah SAW, ya tambayi Manzon Allah SAW game da yin azlu da bayin da suka samu a cikin ganimar yaki; sai Manzon Allah SAW ya ce da shi, “Yanzu kuna yin haka? Ya fi dacewa kada ku yi, domin duk wata rai da Allah Ya kaddara za ta rayu a duniya, sai ta rayu.”  Wannan ke kara nuna mana daukar kaddara da yarda da ita ta fi dacewa a wajen sha’anin haihuwa da ma sauran sha’anonin rayuwa na yau da kullum.
Sai sati na gaba, insha’Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.