Shugaban tsohuwar jam’iyyar PDP Alhaji Bamanga Tukur ya yi gargadin cewa duk wadanda aka zabe su a karkashin jam’iyyar PDP amma suka balle daga cikin jam’iyyar za su yi asarar kujerunsu domin jam’iyyar a dunkule take babu wata baraka da ta samu.
Bamanga Tukur wanda ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, ya ce yana nan daram a matsayinsa na shugaban jam’iyyar PDP.
A cewarsa, “jam’iyyar PDP tana da halastaccen zababben kwamitin zartarwa guda daya ne wanda ke karkashin jagorancina,saboda haka ina kara jaddada cewa duk wata kungiya da ta kira kanta a matsayin kwamitin zartarwar jam’iyyar sojan gona ce, domin haka ina shawartar ‘yan Najeriya, musamman jami’an tsaro da sauran cibiyoyin da ke da alaka da mulkin demokaridiyya da su dauke ta a matsayin haka.’’ Inji Bamanga Tukur.
Bamanga wanda yake wannan bayanin a yayin da sauran shugabannin jam’iyyar suke tare da shi, ya kara da cewa, ‘’Za mu tabbatar an hukunta duk wanda ba a zabe shi ya rike wani mukami a jam’iyyarmu ba kuma ba a ba shi wani aiki da zai yi ba amma ya rika kiran kansa a matsayin wanda yake rike da mukami a jam’iyyar PDP.’’
Ya jaddada cewa jam’iyyar PDP tana da kyakkyawan tsarin magance rikicin cikin gidanta, “domin haka za mu yi duk abin da ya kamata domin mu tabbatar duk wadanda suke yunkurin gurgunta shugabancin jam’iyyar PDP sun girbi abin da suka shuka.’’
Bamanga ya kara da cewa,’’Ina kara jaddada cewa a matsayinmu na wadanda ‘yan Najeriya miliyan 160 suka dora wa amanar daukaka mulkin demokaradiyya a cikin shukaru 14 da suka gabata ba za mu nade hannuwanmu mu zura ido mu bar wadansu marasa kishi su raba kanmu ta hanyar haifar da baraka da rudani a tsakanin jama’a ba.’’
Sai dai kuma da yake mayar da martani, shugaban sabuwar jam’iyyar PDP da wadanda suka balle suka kafa Abubakar Kawu Baraje ya bayyana Bamanga Tukur da cewa dangambara ne kawai wanda ya jahilci siyasar jam’iyya.
Baraje ya nuni da cewa, “ ba mu yi mamaki ba domin ya jahilci siyasar jam’iyya. Duk da haka sanannen abu ne cewa akwai matakai da ake bi domin janyewa ko a ce dan jam’iyya ya rasa kujerarsa, domin haka a wayi gari kawai a ce za a janye wadansu mutane daga kujerunsu alama ce da ke nuna cewa yana fama da jahilci kuma bai cancanci shugabantar jam’iyyar PDP ba.’’
barakar da aka samu a jam’iyyar PDP sai kara fadada take yi a kullum domin har an samu Sanatoci 22 da wadansu ‘yan Majalisar Wakilai guda 57 da suka balle daga tsohuwar PDP suka koma sabuwar PDP da ke karkashin shugabancin Alhaji Abubakar Kawu Baraje.
Baya ga wadannan ‘yan majalisar su 57, ana sa ran wadansu ma za su bi sawunsu ciki har da Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Tambuwal, idan majalisar ta dawo daga hutun da take yi a halin yanzu.Sabuwar jam’iyyar ta bullo ne a sakamakon ballewar da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka yi a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da jam’iyyar ta gudanar da babban taronta na kasa na musamman. Cikin wadanda suka ballen har da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnoni guda bakwai da suka da hada da Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako da Gwamnan Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu da Gwamnan Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmad da Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Ribas Chibuike Amechi da Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido da kuma Gwamnan Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamako.
‘Yan majalisar wakilan guda 57 kuwa sun tsallaka zuwa sabuwar jam’iyyar PDP ne kwana guda bayan wadansu ‘yan majalisar dattawa guda 22 sun balle zuwa sabuwar jam’iyyar.
Haka kuma ‘ya’yan sabuwar PDP din sun bukaci hukumar zabe (INEC) ta kwace rijistar jam’iyyar da ke wurin tsohuwar PDP saboda ta saba wa sashi na 22(d) na tsarin mulki da ya bukaci jam’iyya ta tuntubi ‘ya’yanta kafin ta yi gyara a tsarin mulkinta.Saboda haka ne suka maka tsohuwar jam’iyyar a babban kotun Legas tare da bukatar kotun ta haramta wa Alhaji Bamanga Tukur ci gaba da shugabancin jam’iyyar PDP.
Sun yi nuni da cewa, sun gano an cusa wadansu shedarori da ba a san da su ba a tsarin mulkin da aka yi wa gyaran fuska na shekarar 2012 kuma babban taron jam’iyya bai amince da su ba haka kuma babban kwamitin zartarwa na jam’iyyar, wanda ya sanya tsarin mulkin da suke amfani da shi a halin yanzu ya zama jabu da bai kamata a yi amfani da shi ba.
Haka kuma sun yi nuni da cewa, hatta hukumar zabe ma ba a sanar da ita cewa an cusa wadannan shedarorin ba kamar yadda tsarin mulkin kasar nan ya tanada, wannan ya sanya tsarin mulkin da jam’iyyar PDP ta yi amfani da shi ta gudanar da babban taronta na shekarar 2013 ya zama haramtacce saboda ta yi amfani da tsarin mulki na jabu maimakon sahihin tsarin mulki wajen shirya taron.
Sabuwar PDP din kuma ta yi zargin cewa a watan Mayun shekarar 2001 an kori Bamanga Tukur daga jam’iyyar PDP tare da wadansu mutane bakwai, kuma Alhaji Bamanga bai cika sharuddan da aka gindaya a tsarin mulkin jam’iyya ba da zai sanya ya samu damar komawa cikin jam’iyyar, domin haka halartarsa babban taron jam’iyyar da aka gudanar a shekarar 2012 har aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar cuwa-cuwa ne kuma haramtacce ne domin shi ba dan jam’iyyar ba ne.
A ranar Talata aka yi wani yunkuri domin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar amma saboda gwamnoni bakwai da suka balle sun ki halartar taron dole aka dage zaman zuwa ranar Talata mai zuwa. Kamar yadda shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar Tony Anenih ya bayyana wa manema labarai a Abuja, ya ce an dage taron sulhun zuwa ranar Talata ne saboda gwamnoni bakwai da ke korafi ne suka bukaci a yi haka domin su samu damar tuntubar mutanensu.
Ya ci gaba da cewa, bangaren Bamanga Tukur da fadar shugaban kasa su ma za su yi amfani da dagewar da aka yi domin su nemi shawarar yadda za a magance matsalar: “Daga cikin abubuwan da za a yi akwai taro da za a yi da wadansu shugabannin jam’iyya tare da tsohon shugaban kasa Obansanjo a yau jumu’a da safe, sannan ranar Alhamis kuma a yi taro da gwamnoni. Na amince cewa wadansu daga cikin gwamnonin ya kamata su yi korafi, amma ina fatan da zarar an shawo kan matsalar za su dawo.’’
Sai dai kuma wata majiya ta kusa da gwamnonin bakwai ta nuna cewa gwamnonin ba su da sha’awar su sake wani zama da shugaban kasa dangane da matsalar ce, domin sun yi duk abin da ya kamata kafin su yanke shawarar ballewa, hudu daga cikinsu ne kawai suka halarci taron da aka yi ranar Lahadi da dare.
Aminiya ta gano cewa, mafi yawan gwamnonin da ke korafi sun bar Abuja tun ranar Litinin da yamma domin kada su halarci taron da za a yi ranar Talatar da ta gabata, hakan ne ya sanya dole aka dage taron zuwa wata ranar Talatar. Inji majiyar tamu.
Amma a ranar Talatar shugaban kasa ya yi wani karamin taro da gwamnonin PDP guda 10 da suke biyayya ga Bamanga Tukur, kodayake ba a bar manema labarai su ji abin da ake tattaunawa ba.Gwamnonin da suka halarci taro sun hada da Gwamnan Bauchi Isa Yuguda da Gwamnan Kogi Idris Wada da Gwamnan Delta Emmanuel Uduaghan da Gwamnan Kaduna Mukhtar Ramalan Yero da Gwamnan Binuwai Gabriel Suswam da Gwamnan Abiya Theodor Orji da Gwamnan Kurosribas Lyel Imoke da Gwamnan Bayelsa Henry Dickson da Gwamnan Akwa Ibom da kuma Gwamnan Gombe Ibrahim dankwambo.
Haka kuma akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya Anyim Pius Anyim da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP Uche Secondus da kuma Mai bai wa Shugaban kasa Shawara ta fuskar siyasa Ahmad Gulak.
Sunayen ’yan majalisar wakilai da suka koma sabuwar PDP
1.Abdullahi Balarabe
2.Abdulmummuni Jibrin
3.Ali Ahmad
4.Abdullahi Muhammad Wamako
5.Abdullahi Muhammad Rico
6.Abdulmalik Usman Cheche
7.Adamu Bashir
8.Ahman Patigi Aliyu
9.Ahmad Zarewa
10.Aishatu Ahmad Binani
11.Aiyedun Akeem Olayinka
12. Alhasan Ado Garba
13.Aliyu Madaki
14.Aliyu Shehu
15. Aminu Shagari
16.Aminu Suleiman
17. Aminu Tukur
18. Andrew Uchenud
19.Asita Honorable
20. Bashir Baballe
21. Bleasing Nsiegbe
22. Dakuku Peterside
23.Dawari George
24. Faruq Muhammad Lawan
25.Gibson Nathaniel
26. Gogo Bright Tamunu
27.Haliru Zakari Jikantoro
28. Hassan Adamu
29. Hussaini Namadi
30. Ibrahim Ebbo
31. Ibrahim Tijjani Kiyawa
32.Isa Bashir
33. Kabiru Achida
34.Khabeeb Mustapha
35.Maurice Pronen
36. Muhammad Sabo
37. Mpigi Barinda
38. Muhammad Ahmad Mukhtar
39. Muhammad Ibrahim
40. Muhammad Sani Kutigi
41. Mukhtari Muhammad
42. Musa Ado
43. Musa Sarkin Adar
44. Mustapha Bala Dawaki
45. Mustapha Mashood
46. Ogbonna Nwuke
47.Rafi’u Ibrahim
48. Sa’ad Nabunkari
49.Sani Muhammad Aliyu
50.Shu’aibu Gobir
51. Sokonte Davies
52. Safiyanu Ubale
53. Umar Bature
54. Usman Wada
55. Yusuf Dunari
56. Sule Yusuf Galambi
57. Zakari Muhammad