✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bam ya tashi a wata makabarta a Saudiyya

Hukumomi sun bayyana cewa akalla mutum uku ne suka jikkata yayin da wani abun fashewa ya tashi a wata makabarta a birnin Jedda na kasar…

Hukumomi sun bayyana cewa akalla mutum uku ne suka jikkata yayin da wani abun fashewa ya tashi a wata makabarta a birnin Jedda na kasar Saudiyya yayin da jami’an diflomasiyya na kasashen duniya daban-daban suka taru domin tuna wa da ranar da aka kawo karshen yakin duniya na daya.

Kafar watsa labarai ta Aljazeera ta ruwaito cewa jami’ai daga ofisoshin jakadanci na kasashen duniya daban-daban sun halarci taron da aka gudanar ranar Laraba a makabartar da ba ta musulmi ba domin tuna wa da mamatan da suka mutu a yakin duniya na daya.

Awanni kadan bayan aukuwar lamarin ne mahukunta suka sanar cewa wani dan kasar Girka da wani jami’in tsaro na Saudiyya na cikin wadanda harin ya jikkatar yayin da Gwamnatin Birtaniya ta ce akwai dan kasarta daya da ya samu kananan raunika.

Rahoton da Saudiyya ta fitar yayin bayar tabbacin cewa jakadun kasashe da dama sun halarci taron ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da ofisoshin jakadancin Faransa da Girka da Italiya da Birtaniya da Amurka wadanda dukkaninsu ke da alaka da bikin, sun yi Allah wadai da harin suna mai cewa “harin da matsarota suka kai bai dace ba.”

Gidan talabijin na Saudiyya ya hasko yadda yanayin ya kasance bayan harin da aka kai, sai dai ya ba da tabbacin a kan cewa komai ya lafa.

Har kawo yanzu dai babu wadanda suka yi ikirarin nuna alhakin kai harin.