Tashin bam ya kashe wani yaro dan shekara 13 a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno.
Yaron ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake wasa da wani bam din da ya ki tashi da aka dawo da shi daga karamar hukumar Bama, a ranar Litinin.
Fashewar bam din a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke karamar hukumar Jere ta kuma raunata karin wasu mutum uku.
- ‘Yan bindiga: Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi
- Za a tallafa wa wadanda harin Sokoto ya rutsa da su
- Jami’an tsaro sun kara matsa lamba kan ’yan bindiga a Sokoto
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin.
Sanarwar ta ce wadanda suka samu raunin bam din na samun kulawa a Asibitin Kwararru na Jihar Borno.