Akalla mutum shida ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wata motar matafiya ta taka wani bam a Karamar Hukumar Konduga da ke Jihar Borno.
Ana dai zargin mayakan Boko Haram ne suke binne bama-bama a wata hanya da ta ratsa wani kauye da ke tsakanin Bama da Kawuri a Karamar Hukumar ta Konduga.
- Fitattun ’yan kwallon da suka koma Saudiyya da taka leda
- Karin kudin jami’a ya jefa iyaye da dalibai cikin zullumi
Wata majiya da ta fito daga Zagazola Makama, kwararrer mai fashin baki kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi ne ya bayyana hakan.
Majiyar ta ce wani sabon Kwamandan Boko Haram, Alhaji Ari Hajja Fusam kuma Amir al-Jaysh na kungiyar Jamat Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihd ne ya jagoranci dasa bama-baman tun daga sansaninsu na Gaizuwa da ke da nisan kilomita kadan daga wurin da lamarin ya faru.
Aminiya ta samu labarin cewa daya daga cikin motocin da ke sufuri ce kirar Toyota Starlet da ta taso daga Jihar Adamawa ne ta taka bam din inda ya kashe fasinjoji biyar da ke cikin motar.
Sai dai direban wanda ya samu munanan raunuka, daga baya ya rasu bayan sa’a daya a wani asibiti a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Bayanai na cewa hanyar da ke tsakanin garin Bama da Konduga ta kasance cikin kwanciyar hankali, domin ba a samu wani hari ba a cikin shekaru 6 da suka gabata.
Mazauna Maiduguri sun ce sun yi mamakin yadda al’amura ke faruwa a baya-bayan nan, ganin yadda ayyukan ta’addanci ke kara kamari duk da kiran da gwamnati ta yi na mika wuya.
A bayan nan dai gwamnati ta ce sama da ‘yan ta’adda dubu dari da iyalansu sun mika wuya, amma yawan hare-haren da ake fuskanta a wannan lokuta na nuni da cewa akwai bukatar a kara kaimi kan ayyukan yaki da ta’addanci musamman a jihar Borno.