Rashin nunawa ko samun soyayya daga ma’aurata yana jefa al’umma cikin wani hali na ko-in-kula, musamman ma’auratan da soyayya a tsakaninsu ke gina al’umma ingantaciya, amma sai a iske tun ranar farko zaman hakuri da rashin fahimta da danne zuciya ake yi.
Hakan kan sa wadansu matan gaza samun gamsuwa daga mazansu, ta yadda mazan kan kaurace wa matan, yayin da masu gidan da kan yi ba-zata kan iske abin mamaki a gidaje, kamar a iske matar da ta shaku da mata na nuna iko fiye da mai gidan a wasu lokuta ma takan nemi matar.
Wadansu mazan ba su iya soyayya ba, abin nufi ba su nuna wa matansu so, sai ba da umarni! Yayin da mafi yawancin ’yan matan wannan zamani kan taba rayuwa kafin aure! A haka suna bukatar abubuwa tare da kauna da kula. Rashin gamsar da juna ta sa maza da dama neman wadansu mata a waje, ko abokan aiki ne, inda a magana ma sai su samu kwanciyar hankali, sabanin ta gida bagidajiya ga daga murya da rashin iya tarairaya.
Babban abin bakin ciki anwannan harka da ke yaduwa shi ne, abin ya shafi matan aure, ta yadda za a iya iske matar aure da kawa, ’yar aiki ko dillaliya suna huldodinsu, kuma ba maganar talakawa ko attajirai. Masu irin wannan harkar abokai suke nema don a kulla ta. Ganin ba a daukar ciki ma ya sa matasa kan rungumi wannan harka. Musamman munafukai masu sanya hijabi da nikabi, wadanda kan yi ba duhu!
A irin haka ne wani ya dawo gida ya iske kayan wasan jima’i a falo, yana shiga daki sai ya iske matarsa da kawarta a dunkule, nan take ya suma! Barin mata na zaman kansu kan haifar da madigo, karuwanci da shaye-shaye, musamman a makarantun gaba da sakandare, ta yadda wadansu ’yan matan kan gwammace su sadu da lakcarori a kan karatu a aji duk da cewa ba kowane malami yake yarda ya sadu da dalibansa ba.
A makarantun kudi, masu zaman kansu irin wannan hali bai gushe ba, domin ana samun wake daya wanda zai bata miya! Dole sai an sa ido ko a makarantun jeka-ka-dawo ne, a sa ido a gida a waje. Sau da yawa akan koyi karatu kuma a lalata tarbiyya, wani lokaci ba a karatun, kuma ba a samun tarbiyyar. Akan bi sunan makaranta, da su wa ke makarantar, ba tare da an yi la’akari da malaman ba balle manhajar.
A irin wannan tsarin yara kan koyo tarbiyyar haya, su kawo gida, su gurbata unguwa da kannensu, idan mata ne sai a rika maganar aure da dadi auren kafin shekarun auren daga nan yarinya ta matsu don kebewa da mazinaci, wani lokacin ta rika gaba da wadanda kan hana ta mu’amala da mashiririta.
Sau da yawa iyaye kan matsa wa ’ya’ya da sai sun yi jami’a ko wata makarantar gaba da sakandare kafin aure, abin da kafin a je ko’ina sai su mayar da’yarsu mazinaciya, sun take hakkinta da sunan so da wayewa.
A wasu makarantun malamai mata kan far wa ’yan mata, wani lokacin tun a sakandare kuma a rika rufa-rufa, haka akan samu kato ya shigo makarantar mata domin ba a kange makarantun ba. A gidaje ma ba a bar wannan fasadin ba, inda ake wa kanne, ’yan biki, ’yan hutu, ko a yi fyade kamar yadda ake a sakandare daga fyade har ya zama jiki.
Wani abin takaici ga masu bincike shi ne wannan harkar dama cikin sirri ake yin ta, saboda haka gane abin boyen yana da wuya, musamman sirri a tsakanin mata. Makarantun mata kadai, na kwana ko jeki-ki-dawo sun zama sansanonin wannan fitina, domin babu mazan da za su neme su, sai su nemi juna!
Buhari Daure
Kofar Kaura, Katsina.