Wannan ne ci gaban mukalar daga Babban Lauya, Ustaz Yusuf O. Ali (SAN), fassarar Barista M. B. Mahmoud Gama:
A wannan gabar, bari mu dan yi shiftar wasu kunshin dokoki da suka yi magana a kan wannan mummunan laifi don mu sake fahimtar nauyinsa.
- An tsinci gawar yarinyar da aka yi wa fyade a makabarta
- Ta gutsure mazakutarsa bayan ya yi mata fyade
- Balahirar Fyade: Jan hankali ga iyayen yara da al’umma (1)
Sashi na 218 na Kundin Laifuffuka na Kasa ya daddale cewa: “Duk mutumin da ya yi wa yarinya ’yar kasa da shekara 13 fyade, to ya aikata babban laifi, wanda hukuncinsa shi ne daurin rai-da-rai a gidan yari”.
Sashin ya ci gaba da cewa, “kuma duk mutumin da ya yi yunkurin aikata fyade (ko bai aikatan ba) ga yarinya ’yar kasa da shekara 13, to shi ma, ya aikata babban laifin da zai jaza masa zaman gidan yari har na tsawon shekara 14”.
Dokokin da aka tanada don dan bunburuntu a yanar gizo (Cyber Crime Prohibition, Prebention etc Act) na 2015, sun zayyano ayyukan da ke kaiwa zuwa ga aikata fyaden; inda suka ce duk mutumin da, da niyya yake amfani da kwamfuta ko ta hanyar sadarwa ta kwamfutar: “(a) wajen kirkirar bidiyon batsa, ko (b) wajen tallata ko yada bidiyon batsa na kananan yara, ko (c) wajen rarraba ko tura bidiyon batsa na kananan yara, ko (d) wajen nemo bidiyon batsa na yara don kallo ko nemo wa wani don ya kalla, ko (e) wajen mallakar hotuna ko bidiyon batsa na yara a cikin kwamfuta ko adana su a cikin kwamfutar”. To ya aikata laifi a karkashin Sashi na 23 na Kundin Laifuffuka na Cyber Crime Act, 2015.
Har ila yau, a karkashin Sashi na 23, Karamin Sashe na (3), dokar ta ci gaba da cewa, duk mutumin da, da gangan ko da ganganci, ya gabatar da kansa ga yarinya; ko yake neman ta ta hanyar kwamfuta (a nan wayar hannu ma kwamfuta ce), don ya hadu da ita “(a) don yin jima’i da ita, ko (b) don yin jima’i da ita ta hanyar: (i) yin amfani da karfi ko tsoratarwa ko yaudara, ko (ii) yin amfani da wata dama ko iko ko matsayi ko amincewa (irin ta ’yan uwantaka), ko (iii) yin amfani da wani yanayi da yarinyar ta samu kanta a ciki; kamar gushewar hankali ko nakasa ko kasancewar tana karkashinsa (wajen kula da ita), ko
(c) don sanya ta cikin harkokin batsa don samun wata riba, ko kuma tilasta mata don samun wata fa’idar ta daban”. To wannan mutumin ya aikata laifi da ke karkashin wannan sashi na Kundin Cyber Crime Act, 2015.
Hakkin iyaye da al’umma wajen kula da yara
Babu ko shakka, iyaye na da babban tasiri ga rayuwar ’ya’yansu. Saboda haka, iyaye tamkar wata fitila ce mai haska musu gaba cikin rayuwarsu dukkanninta.
Fahimtar haka ce ta sa a karkashin Sashi na 14 na Kundin Dokokin Hakkin Yara, ya samar da cewa kowane yaro/yarinya na da hakkin samun Kulawar Iyaye, da ba su kariya daga kowace irin cutarwa, da kuma daukar nauyin rayuwarsu.
A Sashi na 14, Karamin Sashi na (2) na dokar ya ci gaba da cewa: “kowane yaro yana da hakkin samun kulawa daga iyayensa, ko wadanda Allah Ya dora wa hakkin kulawa da shi, gwargwadon ikonsu.
“Sannan a duk lokacin da ya dace, yana da ikon ya nemi wannan hakki nasa a kotu”.
Shi kuwa Sashi na 2 na kundin, fadada masu ba da kulawar ya yi tun farko, inda ya ce, dole ne ya samu waccan kulawar daga iyaye, ko masu kula da shi, ko al’umma da hukumomi da kungoyoyi da hukumomin da aka yi su, musamman don kula da yara. Duk fa don samun kyautatuwar rayuwar su yaran.
Sannan duk wadannan hukumomi da kungiyoyi da dokar ta zayyana su a sama, to tilas su ba da kulawar ta fuskar ba su natsuwa da ingantacciyar lafiya da walwala, gwargwadon yadda dokokin da suka kafa hukumomin da kungiyoyin suka tanada.
Daga nan sai Sashi na 11 na kundin ya dora da cewa: “kowane yaro yana da hakkin a kare masa mutuncinsa a matsayinsa na mutum kuma kare mutuncin nasa na nufin dole ne kada a cutar da shi ta fuskar:
(a) jikinsa ko hankalinsa, ko wulakanta shi ko aikata masa babban laifi kamar fyade, ko (b) azabtar da shi ta fuskar nuna masa rashin jinkai –wai– don hukunta shi, ko (c) ci masa mutunci ba-gaira-ba-dalili, ko (d) iyaye ko wadanda suke kula da shi da kungiyoyi ko hukumar makaranta ko wani da yake da iko da shi yaron, tursasa shi yin wani aiki mai kama da bauta”.
Daga nan sai Kundin na Dokokin Hakkin Yara, tun daga Sashe na 15 Karamin Sashi (1) zuwa Karamin Sashe na (7), ya yi tilawar hakkin da yara ke da shi wajen iyaye da hukumomi don ba su ilimi tun daga matakin firamare har zuwa babbar sakandare.
Kuma dokar ta tanadi hukunci ga duk mahaifin da ya gaza sauke wannan hakki da gangan.
Duba ga dokokin kawai zai tabbatar wa da mai karatu cewa, lallai iyaye da wadanda Allah Ya dora wa hakkin kula da yaran da kuma al’umma baki daya, akwai hakkoki da dama da suka ratayu a wuyansu, tun daga ciyarwa, tufatarwa, samar da muhalli da ba da kulawa, da ilimanatarwa da tarbiyantarwa, da sauransu, da dokokin suka nemi da su sauke su, idan kuwa hakan ba ta samu ba, sai dokokin suka yi tanadin hukuce-hukunce masu tsauri da za su fada a kan duk mahaifin da bai cika su ba.
Yawaitar Fyade A Najeriya
Yawaitar aukuwar fyade a Najeriya ya zama wani tabbataccen batu abin tattaunawa a tsakanin ’yan Najeriya a yau.
Wannan ba ya rasa nasaba da irin cigaban da aka samu na hanyoyin yadawa da tattaunawa a kan labarai da suka shafi fuskokin rayuwa daban-daban ta al’umma.
Wadannan kafofin yada labarai sun hada da kafofin sada zumunta na zamani, kamar WhatsApp, Facebook, Istagram, da sauransu, da kullum suke mayar da labaran da aka saba jin su da wai-wai zuwa tabbatattun labarai ko akasin haka.
Wannar aika-aika ta fyade, ta fi fadawa kan mata da kuma kananan yara.
Kuma ba zai zama mun yi karin gishiri ba idan muka ce cikin mutanen da suka fi aikata wannan laifi sun hada da masu kudi da talakawa, da masu ilimi da wadanda ba su yi karatu ba, da ma’abota addini (a zahiri) da wadanda ba ruwansu da addini, da kuma wadanda suke rike da madafun iko, ko wadanda aka damka wa amanar su matan ko yaran.
Wadanda kuma za ka samu su ke aikata wa matan da kananan yara wannan ta’annati, a mafi yawan lokuta kuma abin takaici, su ne iyaye su kansu da malaman makaranta da fasto-fasto da masu gidajen haya da direbobi da sauransu.
Za mu ci gaba