Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya kafa kwamitin binciken zaluncin jami’an ‘yan sanda na SARS a jihar.
Gwamna Bala ya kafa kwamitin ne a ranar Laraba domin bincikar laifukan ‘yan sanda a jihar biyo bayan korafe-korafe da jama’ar jihar suka shigar gaban gwamnatin jihar, bisa laifukan da suka shafi zalunci da cin zarafin al’umma.
- Lalong ya kaddamar da kwamitin binciken zaluncin SARS
- Zalunci: An fitar da sunayen ’yan sandan da za a hukunta
- Kwamitin binciken cin zalin ‘yan sanda zai fara zamansa a Legas
- Gwamnatin Bauchi ta bankado ma’aikatan bogi 2,116
Gwamnan ya bawa kwamitin tsawon watanni shida ya gudanar da binciken tare da gabatar masa da sakamako domin daukar matakin shari’a da ya dace.
Kwamitin karkashin jagorancin tsohon Mai Shari’a Habibu idris a matsayin shugaba, sai tsohon Shubagan Hukumar ‘Yan Sandan jihar CP Hamisu Makama da kuma sauran masu ruwa da tsaki a jihar daga kungiyoyi masu zaman kansu a matsayin mambobi.
Ana sa ran kwamitin zai fara gudanar da aikinsa daga mako mai zuwa domin samar da sakamakon bincikensa a kan lokaci.