✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda bakuwar cutar tumatir ke jawo wa manoma asara a Filato

An kasa gano abin da ke kawo bakuwar cutar tumatir a Filato.

Manoman tumatir a Jihar Filato na kokawa kan bullar wata bakuwar cutar tumatir da ke lalata musu amfanin din da suke shirin fara cin amfani.

Manoman da suka ce bakuwar cutar na barazana ga alherin da suke sa ran samu idan suka girbe tumatir dinsu, sun ce sun sa duk magunguna cutar tumatir da suka sani amma abin ya ki ci, ya ki cinyewa.

Wasu daga cikinsu sun ce lamarin ya kai ga har sun tuntubi kwararru domin magance matsalar, amma abin ya faskara.

Yadda bakuwar cutar take

Daya daga cikin manoman ya shaida wa wakilinmu cewa cutar na farawa ne bayan tumatir ya fara yin ’ya’ya, inda ganyensa ke yin yaushi, ’ya’yan kuma su koma ruwan kasa wasu kuma su yi digon baki-baki a jikinsu.

Daga nan kuma sai tumaturin ya rube, ba za a iya amfani da shi ba.

Duk da cewa manoman sun ce ba su san na yi ba kan bakuwar cutar, shugaban kungiyar manoman tumatir a Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, Auwal Tanko Haruna, yana zargin rabar da ke sauka da dare ce musabbabi.

Ya ce ya kai samfurin ’ya’yan tumatirin da suka kamu da cutar ofishin shirin aikin noma na FADAMA 2 da ke Jos, babban birnin jihar, domin a yi gwaji, inda aka ce ya koma a makon gobe domin karbar sakamako.

Shugaban manoman ya ce a bara kadai sun samu kwando sama da 200,000 na tumatir a yankin, amma bana ba su da tabbacin samun wani abin a zo a gani, saboda bullar wannan bakuwar cuta.

Ya ce bullar cutar ta dagula wa manoman lissafi, domin ba su san abin da za su yi ba wajen magance ta.

Amma duk da haka idan aka gano bakin zaren, za su iya noma sabuwa har su girbe kafin watan Janairun 2022.

Don haka ya yi kira ga shugabanni a karamar hukumar da su taimaka  musu wajen shawo kan matsalar, domin yanzu asara suke yi na kudaden da suka kashe a kan abin da suka shuka.

Ya kuma bukaci manoman da su kwantar da hankalinsu tare da fatar za a gano bakin zaren a kuma magance bakuwar cutar da ta addabi amfanin gonarsu.

Wani manomin tumatir a unguwar Lamingo da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Marcel Ndubuisi, ya ce ya yi asarar kusan duk tumaturin da ya shuka bayan ya yi duka abin da zai iya ba tare da samun maganin cutar ba.

Ndubuisi ya ce har kwararru ya dauko suka gudanar da bincike a gonar tasa, amma ba su iya gano mece ce matsalar ba.

A cewarsa, wasu na ganin cutar na da alaka da sauyin yanayi, a yayin da wasu ke ganin gubar kasa ce ta shafi amfanin shukar.

Ya ce an shawararce shi da bar gonar tasa ya koma wani wuri, amma hakan na da tsada sosai kuma ba ya tunanin mafita ce domin a wasu wuraren ma ana fama da cutar.

A cewarsa, samun rancen banki na gagarar su a halin yanzu, ko sun samu bankunan da ke bayar da bashin na so ne a biya su kafin manoman su girbe amfanin gonarsu, wanda kuma abu ne mai wuya.

Manomin ya ce duk da cewa suna noman rani ne a kusa da wani dam, amma yanzu farashin injin ban ruwa ya tashi daga N30,000 yana kaiwa har N75,000.

Ndubuisi ya ce wadannan matsalolin sun jefa manoman tumatir a cikin tsaka mai wuya, amma suna fata hukumomi da masu fada a ji za su kawo musu dauki.