A Yammacin ranar Talata ne Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayar da tabbaci kan mutuwar wasu mutum hudu da kuma mutum 24 da aka kwantar a asibiti sakamakon wata bakuwar cuta da ta bulla a yankin Helel da ke birnin Shehu.
Gwamnan cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannunsa, ya bayyana damuwa da alhini a yayin da yake mika ta’aziya ga ’yan uwan wadanda suka yi rashi.
- Cutar COVID-19 ta yi ajalin mutum 15 a Najeriya, 1,303 sun kamu
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4 tare da raunata wasu
- Abin da ’yan Najeriya ke bukata daga Sabbin Hafsohin Tsaro
A cewarsa, an kafa wani kwamitin kwararru da nufin bin diddigin wannan bakuwar cuta don nemo maganinta da gano dabarun dakile ta.
Sanarwar ta ce, “Mun samu labarin cewa wata bakuwar cuta ta yi ajalin mutum hudu a yankin Helele na Jihar kuma a halin yanzu akwai mutum 24 da aka kwantar inda suke samun kulawar mahukunta na lafiya a asibitoci daban-daban da ke fadin Jihar.”
“Gwamnatin jihar ta kafa wani kwamitin kwararru karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiyar Jihar domin gudanar da bincike a kan wannan bakuwar cuta domin gano maganinta da kuma yadda za a dakile ta.”
“Doriya a kan haka, Gwamnati ta dauki nauyin kula da lafiyar wadanda a halin yanzu suke jinya sakamakon kamuwa da cutar, sannan tana musu fatan samun sauki domin komowa cikin ’yan uwansu da makusanta,” a cewar sanarwar.
Kazalika, Gwamna Tambuwal ya kirayi al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, inda ya nemi su dabi’antu da al’adar tsaftace kawunansu da kuma mahalli tare da dagewa wajen gudanar da addu’o’i a wannan mawuyacin hali da ake fuskanta.