✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Bakin kishi ya sa na kashe ’yar kishiyata’

A makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta gabatar da wata mata mai suna A’isha Abubakar da ke Sabuwar Unguwa a Karamar Hukumar Rimi…

A makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta gabatar da wata mata mai suna A’isha Abubakar da ke Sabuwar Unguwa a Karamar Hukumar Rimi da ke jihar, bisa zarginta da kashe ’yar kishiyarta ta hanyar zuba mata guba a cikin abinci.

Kakakin Rudunar, Sufuritanda Gambo Isa ne ya gabatar da wadda ake zargin ga manema labarai a madadin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Sanusi Buba, inda ya ce yarinyar da aka kashe, wadda ita ma sunanta A’isha, mai kimanin shekara uku, ita ce ta biyu a wajen mahaifiyarta Hadiza. Hadiza ita ce amarya daga cikin mata hudu da Malam Abu Fardami Mai Gyaran Fanfo, ma’aikaci a Karamar Hukumar Rimi yake aure

Da take bayyana yadda abin ya faru ga ’yan sanda, A’isha ta ce marigayiyar na cin abinci tare da ’ya’yanta biyu, Maf’ula da Ibrahim, inda ta yi amfani da wannan dama ta zuba guba a gabanta kuma ta hana ’ya’yanta su ci gaba da cin abincin. Ta ce su bar wa A’isha ta ci ita kadai.

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.