Fadar Shugaban Kasa ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi a sakonsa na sabuwar shekara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Obasanjo ba zai taba daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina bakin ciki kan duk wani shugaba wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban kasa ba.
- An kai wa Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta kasa hari
- Yadda dubban mutane suka yi dafifin bankwana da gawar Pelé
Fadar Shugaban Kasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala Gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alkawura a kanta.
Haka kuma Fadar Shugaban Kasar ta ce Obasanjo ya yi wa Kudu maso Gabashin Najeriya karya domin ya samu kuri’unsu, amma Shugaba Buhari bai samu kuri’unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.
Fadar Shugaban Kasar ta kuma ce Obasanjo yana bakin ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da’awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zabe fiye da wanda ya kawo sa kan karagar mulki.
Haka kuma fadar ta zargi Obasanjo da lalata dimokuradiyya a Najeriya bayan kitsa tsige wasu gwamnoni a kasar da suka hada da Joshua Dariye da Rashidi Ladoja da Peter Obi da Chris Ngige da Ayo Fayose.
Wannan martanin na fadar shugaban Najeriya duk na zuwa ne bayan tsohon Shugaban Kasar ya ce Peter Obi ne zabinsa a zaben 2023 haka kuma Obasanjon ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari.