Editan Aminiya mai isar da koken talakawan Najeriya, don Allah ka ba ni dama in koka kan yadda hukumar samar da wutar lantarki ta yanke wa al’umma Naira dubu uku a kowane wata. Shin Edita ka tambaye su, yaya za a yi gidan talaka mai fanka daya tilo da kwayayen da ba su taka kara sun karya ba, zai biya kudi guda da gidan mai kudin da ke da gida cike da na’urorin lantarki masu dimbin yawa. Lallai a rika amfani da ma’aunin mita da zai tantance yawan wutar da mutum ya sha. Idan da hali a bai wa kowane talaka kyautar mita mai kati ko kuma a kan farashi mai rahusa. Da zarar an yi wa talakawa tsari mafi inganci, to za su tabbatar da cewa, wannan gwamnatin ta Buhari ta kawo sauyi fiye da yadda wadda ta kauce ta azabtar da al’umma, domin ba ruwansu da talaka. Saboda haka Baba Buhari ya gargadi hukumar samar da lantarki kan lallai ta yi wa talaka adalci wajen biyan kudin wuta. Daga Baba Ali Sulaiman, Yalwa G/Dutse, Kano 08038823636
Bai kamata talaka ya biya Naira 3000 kudin wuta ba
Editan Aminiya mai isar da koken talakawan Najeriya, don Allah ka ba ni dama in koka kan yadda hukumar samar da wutar lantarki ta yanke…