Bayan Hamdala da Taslimi:
Ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah Mai girma da daukaka. Domin tabbas, babu tsira a nan duniya da gobe Qiyama face sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shi ne ginshiki da tushen duk wani alherin duniya da Lahira.
Ya ku bayin Allah, ya ku ’yan Najeriya! Ya kamata mu tuna cewa a yanzu, muna ta kara kusantar zaben 2019, ga wanda Allah Ya yi wa tsawon rai daga cikinmu. Don haka, idan ba mu ji tsoron Allah, muka yi wa kanmu kiyamullaili, muka yi abin da ya kamata na zaben nagartattun shugabanni masu imani da tsoron Allah, a kowane matakin shugabanci ba, to ina tabbatar muku (Allah Ya kiyaye) cewa abin da muke ji ko gani a yau na bala’in talauci da yunwa da kunci da tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyaki da rashin iya shugabanci da rashin aikin yi ga matasanmu da yin sako-sako da muhimman al’amura da gasa wa talaka aya a hannu da wulakanta ma’aikata da rashin daukar shawara da rashin ababen more rayuwa da talakawa za su amfana da taurin kan masu mulki za su zama wasan yara. Kuma ba korafi ba, wallahi idan ba mu yi hankali ba, sai mun yi mummunar da-na-sanin da ba mu taba yi ba. Allah Ya sauwake, amin.
Ya ku jama’a! Yanzu ke nan, suna neman a sake zabensu, suna neman kuri’un jama’a, amma sun mayar da talakawa ba komai ba, ina ga sun sake dawowa mulki, a lokacin da suka tabbatar da cewa suna zangon karshe na mulkinsu ba za su dawo ba?
Ga shi nan dai duk abin da muke ta kokarin gaya wa mutane ya fito baro-baro. Kowa yana kallo da jin abin da ke gudana a wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Saboda haka, yanzu ya rage mana, kodai mu sadaukar da duk abin da Allah Ya hore mana na ilimi da dukiya da karfi da lokaci da wayo da dabara da hankali da gogewa da iya siyasa da sauransu, mu samar da shugabancin da dukanmu za mu amfana, talaka ya san ana yi dominsa, ’yan kasa su wadata, arziki ya yalwata ko’ina, kayan masarufi ya samu, a yi maganin zaman banza ga matasanmu, a dada samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa; mu ceto kasar nan daga shugabanci na rashin kwarewa ko dukanmu mu yi da-na-sani.
Idan muka ci gaba da zama wawaye, makafi, dibgaggu, marasa kishin kasa, marasa kishin al’umma da kawunanmu, muka ci gaba da yarda da farfagandar karya, to ya rage namu!
Saboda haka, ’yan siyasa da sarakuna da limamai da masu wa’azi da fastoci da ma’aikatan gwamnati da ’yan kasuwa da shugabannin al’umma da talakawa da jami’an tsaro, ku sani hakkin ceto kasar nan ya rataya a wuyan dukanku. Ku manta da kwadayin abin duniya, ku manta da bambance-bambance, ku manta da maganar bambancin jam’iyya, ku manta da duk wata farfagandar karya, mu hadu mu yi aiki tare, domin ganin wannan kasa tamu mai albarka ta dawo mai mutunci, mai yalwar arziki da zaman lafiya da hadin kai da kwarjini a idon duniya.
Ku sani, bala’i da talauci da masifa da yunwa da kunci da rashin biyan albashi da rashin hanyoyi masu kyau da rashin magani a asibiti da rashin ingantaccen ruwan sha da ilimi da rashin tsaro, babu ruwansu da kai wane ne. Babu ruwansu da kai Musulmi ne ko Kirista, babu ruwansu da kabilarka ko jiha ko yankin da ka fito.
Ya ku ’yan Najeriya! Don Allah ku kalli yadda kasarmu ta zama a yau, ku kalli yadda abinci ya gagari magidanci, mutane suna ta kashe kawunansu saboda talauci da kunci, ku kalli yadda talakawa suka kasa daukar nauyin ilimin ’ya’yansu da yadda mutuncin jama’a ke ta zubewa, an mayar da mutane mabarata, ’yan maula, maroka, mayunwata da karfi da yaji. An rufe iyakar kasa, bayan an kasar ba ta da karfin ciyar da kanta, ba ta da karfin dogaro da kanta. Kuma an ce za a fitar da abincinmu zuwa kasashen waje, alhali mu gida ba mu koshi ba, muna cikin yunwa! Arzikin da Allah Ya azurta kasa da shi, an rike an ki saki domin kowa ya amfana. Ku kalli yadda ake tafiyar da shugabanci, sakamakon sakaci da rashin tausayi da rashin imani da rashin daukar shawarwarin kwarai da rashin iya shugabanci. An sakar wa wadansu mutane tsirari harkar gwamnati, an wayi gari sai abin da suka ga dama ake yi. Mutane sun sadaukar da lokacinsu da dukiyarsu da rayukansu da iliminsu da duk abin da Allah Ya hore musu, domin kawar da bakin mulkin gwamnatin Goodluck Jonathan, da suke ganin ba ta kyautata musu. Babban burin mutanen shi ne Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Qasa, wadansu sun mutu, wadansu sun rasa hannu ko kafa, wadansu sun samu matsala da mutanensu duk saboda Buhari. Talakawa sun ba shi gudunmawar kudadensu, amma sai ga shi yau an wayi gari mutane suna da-na-sanin abin da suka yi, domin sun gano wadansu sun karkatar da akalara gwamnatin ba ta iya tabuka musu komai. Canjin da aka yi alkawarin za a samar musu ya zama na bogi da yaudara!
Ko yaki da cin hanci da rashawar da ake magana, mutane sun gano siyasa ce. Domin abokan adawa kawai ake yi wa bi-ta-da-kulli, amma shafaffu da mai, sai abin da suka ga dama suke yi.
Shin ya ku jama’a, za mu ci gaba ne da dora maslaharmu a saman maslahar al’umma baki daya, don kawai tsoron wadansu mutane, ko don gudun zagi? Shin Allah bai umarce mu da mu zama masu adalci ba? Shin da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi ba daidai ba, ba mu yi magana ba? To wannan ma idan ta kauce hanya ba za mu zama adalai mu fito mu yi magana ba kamar yadda muka yi a waccan gwamnati? Ta yaya za mu yi ta cika masallatai da coci-coci kullum da sunan ibada da sunan mu masu addini ne, mu na Allah ne, amma hakan na neman ya zama banza, ya zama munafunci, saboda nuna kabilanci da bangaranci? Kullum mu ne kan hanyar Makkah da Madinah domin yin Hajji da Umara. Kullum mu ne kan hanyar Jerusalem domin yin ibada, amma mun kasa zama adalai da za mu yi wa kowa adalci. Mun kasa hada kai mu tabbatar da shugabanci nagari da kowa zai amfana a kasarmu! An wayi gari kullum kasarmu tana neman zama abin dariya a idon duniya. Shin mun manta cewa dukanmu za mu mutu mu bar abin da muka tara a nan duniya ne? Mun manta ne za mu tashi a gaban Allah gobe Qiyama mu amsa tambayoyi kan yadda muka aiwatar da rayuwarmu a duniya ne? Haba ’yan uwana ’yan Najeriya masu albarka, don Allah me ke damunmu ne?
Ya ku ’yan Najeriya! Ku sani, lallai shekarar 2019 idan Allah Ya sa muna raye, ita ce shekarar da za mu gane cewa shin mun yi hankali ko kuwa har yanzu muna nan gidadawa, wawaye, sako-tumaki-balle jaki? Ita ce shekarar da za mu gane mun koyi darasi a jin jikin muke yi da bakar wahala da tsadar rayuwa da tsadar kayan masarufi da muke fama da su, ko har yanzu ba mu gane komai ba? Ita ce shekarar kwatar kai, idan har ba mu canja wannan halin ba, to, babu lokacin da za mu iya samar da wani abin a zo a gani. Allah Ya kiyaye!
Ya ku ’yan Najeriya! Lallai mu sani, gyaruwar al’umma ta ta’allaka ne a kan gyaruwar shugabanninta, kuma lalacewar al’umma ta ta’allaka ne a kan lalacewar shugabanninta. A duk lokacin da shugabanni suka zama na kirki, masu kishin kasa da al’ummarsu, masu shawartar mutanen kirki, masu daukar shawara, masu tausayi da imani, to ana sa ran mutanen kasa su zama na kirki. Haka duk lokacin da shugabanni suka zama tambadaddu, masu yin sako-sako da al’amurra, ba su iya tabuka komai a kan muhimman al’amurra, suka kasa cika wa jama’a alkawurran da suka dauka na samar da kyakkyawan canji, to lallai ’yan kasa ma haka za su kasance. Domin a inda akuyar gaba ta sha ruwa, dole ta baya ma idan ta zo nan za ta sha. Shi ya sa Musulunci ya ba da muhimmanci sosai a kan sha’anin shugabanci, ya nuna cewa shugabanni dole ne su zamo mutanen kirki ba ashararai ba, adalai ba azzalumai ba, masu iya daukar matakin da ya dace, a duk lokacin da ya dace, kuma ko a kan wa ya dace. Su zamanto su ke tafiyar da ragamar mulkinsu, ba su sakar wa wadansu tsirarin mutane ba. Yin haka zai sa zaman lafiya da ci gaba da arziki da wadata da walwala su yawaita a kasa, soyayya da kaunar juna su watsu, sanadiyyar haka a kawar da kiyayya a cikin zukatan ’yan kasa, ya kasance jama’a ba sa tunanin an mayar da su saniyar ware, domin suna da gwamnati mai bai wa kowa hakkinsa, mai sauraren kowane bangare na al’umma.
Mu ’yan Arewa, ya kamata mu shiga taitayinmu, ya kamata mu yi karatun ta-natsu, ya kamata mu farka daga dogon barcin da muke yi, mu tambayi kawunanmu, shin don Allah Arewa ta amfana da wannan mulkin kamar yadda bangaren Kudu maso Yamma ke amfana? Shin Bola Tinubu ya fi duk wani dan siyasar Arewa ne? Shin kuri’un da Buhari ya samu a Arewa ya same su a yankin Yarbawa ne? Kuma shin me ya sa ne Ministar Kudi take kokarin wulakanta Arewa da ’yan Arewa da hadin bakin su Tinubu da ’yan uwanta, amma Buhari ya yi shiru yana kallo ya kasa cewa komai? Abin da ya faru kwanan nan na dakatar da Alhaji Munir Gwarzo (dan Arewa) daga aiki domin ya dauki matakin da ya dace a kan kamfanin mai na su Tinubu, wato Oando, ya isa misali. Sannan matar nan (Ministar Kudi), idan aiki ya shafi Arewa sai ta ki fitar da kudi domin a yi aikin, amma idan aiki ya shafi yankinsu na Yarbawa sai ta fitar da kudin nan take. Kuma duk muna kallo mun yi shiru!
Kwanan nan gwamnatin Buhari ta hannun Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), ta wulakanta kamfanin dan Arewa, Alhaji Atiku Abubakar, wato Intels, amma duk ba mu damu ba. Sai ga shi an dakatar da dan Arewa daga mukaminsa, saboda ya dauki matakin da ya dace a kan kamfanin su Tinubu na Oando!
Ko maganar da gwamnatin Buhari ke yi na samar wa matasa aikin yi na N-Power, don Allah mu bincika, su wane ne suka fi amfana, ’yan Kudu ko ’yan Arewa? Me ya sa muke yaudarar kawunanmu ne? Me ya sa ba za mu fada wa juna gaskiya ba? Me ya sa za mu munafunci kawunanmu? Sannan don Allah ku lura da kyau, za ku ga cewa, duk wani al’amari na ’yan Arewa, Buhari ba ya ba shi wani muhimmanci, ya fi ba da muhimmanci ga sha’anin ’yan Kudu. Aure ne, mutuwa ce, ta’aziyya ce, jaje ne, ziyara ce, taron harkokin addini ne, sam na ’yan uwansa ’yan Arewa da suka sadaukar da rayukansu saboda shi, bai dame shi ba. Amma ku kalli yadda Mataimakinsa Osinbajo yake shiga jama’arsa don Allah!
Imam Murtada Gusau, shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da Masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene da ke Okene, Jihar Kogi. Kuma za a iya samunsa ta waya mai lamba: +2348038289761.