A watan da ya gabata ne Shugaban Hukumar Kwastam Hameed Ali ya bayar da umarnin rufe gidajen mai a garurruwan da ke kilomita 20 da kan iyakokin kasar nan da nufin magance matsalar fita da man man fetur da ake yi ba bisa ka’ida ba (fasa-kwauri).
Hukumar Kwastam ta bayar da wannan umarnin ne a wata takardar sanarwa da ta fitar a ranar 6 ga Nuwamba, inda ta nuna cewa Shugaban Hukumar Hameed Ali ya haramta sayar da mai a gidajen man da ke garurruwan da ke kilomita 20 a kan iyakokin kasar nan, kuma ba a yarda a sauke mai a wadannan gidajen mai ba komai kankantarsa.
Tun lokacin da Hukumar Kwastam ta fitar da wannan sanarwar aka yi ta cece-ku-ce a kai, wadansu na ganin ba a kyauta ba, wadansu kuma suna ganin an yi daidai.
Abin lura a nan shi ne, idan har ana so ne a yi maganin fasa-kwaurin mai, kamata ya yi Hukumar Kwastam ta yi kokarin gano hanyar da za ta kama masu fasa-kwaurin, maimakon ta yi wa mazauna yankunan fyadar ’ya’yan kadanya, duk ta hukunta su ta hanyar azabtar da su.
Mutanen da ke zaune a wadannan garurruwa na kan iyaka ba su suka zabi zama a wadannan garuruwa ba, ita kanta Najeriya ce ta same su a wuraren har aka ce sun zama al’umma a yankin Najeriya. Kuma kasancewarsu a bakin kan iyaka bai sanya sun zama daban da sauran ’yan Najeriya ba, su ma ’yan Najeriya ne cikakku kamar sauran ’yan kasar nan, kuma wajibi ne gwamnati ta tsare rayukansu da lafiyarsu da dukiyoyinsu da mutuncinsu da sauransu.
Amma wannan mataki da gwamnati ta dauka na hana sayar da mai a wadannan garurruwan kamar yana nufin ana neman ganin iyakar al’ummomin da ke zaune a kan iyakar kasar nan ne, domin bai kamata a hukunta dimbin mutane saboda laifin mutane kalilan ba.
Wannan matakin da Hukumar Kwastam ta dauka talakawa masu karamin karfi ne zai fi shafa, domin rahotanni sun nuna cewa sakamakon wannan mataki da aka dauka farashin mai a garurruwan da ke yankunan ya yi tashin gwauron zabo, an ce har Naira 600 ana sayar da litar mai a wasu wuraren.
Ya kamata gwamnati ta yi tunani cewa man nan fa yanzu dole ne a rayuwa, domin a sakamakon karancin wutar lantarki mutane sun koma suna amfani da janareta ne wajen gudanar da sana’o’insu, saboda haka masu kananan sana’o’i irin su teloli da masu walda da masu injin nika da masu facin tayoyi da sauransu suna bukatar man fetur domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum, ban da wadanda za su saya domin amfani da shi a janaretocin gidajensu saboda maganin zafi da sauro.
Yanzu da aka hana sayar da mai an jefa dimbin mutane a cikin wahala, domin masu sana’o’i da yawa za su gurgunce saboda ba za su iya sayen man fetur da tsada ba, idan kuma sun iya saye, kayan da za su samar zai yi tsada har a kasa saye.
Su kansu gidajen man da aka rufe, ba masu gidajen man kawai zai shafa ba, zai shafi ma’aikatan gidajen man da sauran talakawa da suke sayar da kayayyakinsu a gidajen man domin su samu abin da za su rufa wa kansu asiri.
Bai kamata a ce gwamnati ta yi watsi da mawuyacin halin da talakawan da ke wadannan yankunan za su shiga ba saboda laifin wadansu masu hannu da shuni, hasali ma dai ai ana kara wa masu karfi karfi ne saboda su ne za su nemo man a wasu wuraren su sayar wa talakawa da dan karen tsada. Talaka dai shi ne sha-wuya.
A wannan lokaci da ya kamata gwamnati ta himmatu wajen samar wa mutane aikin yi, bai dace a ce ta koma tana kassara wadanda suka yi kokarin samar wa kansu sana’o’in da za su rufa wa kawunansu asiri ba.
Idan aka duba da idon basira za a ga cewa wannan mataki na Hukumar Kwastam ya fi musguna wa yankin Arewacin kasar nan, domin mafi yawan garurruwan da matakin ya shafa a yankin Arewa suke.
Ana ta bayanin cewa talauci ya yi kanta a yankin Arewacin kasar nan, amma maimakon a taimaka a rage wa mutane radadin talaucin sai ma kara tunkuda su cikin talaucin ake yi, domin babu yadda za a yi tattalin arzikin al’umma ya bunkasa idan gwamnati ta yi watsi da halin da suke ciki ta mayar da hankali wajen daukar matakan da za su gallaza musu.
Ko kwanan nan Bankin Duniya ya fitar da sanarwar da ta nuna cewa kashi 25 na fakiran da ake da su a duniya a yankin Arewacin Najeriya suke. Dole ne talauci ya samu gindin zama a yankin Arewa saboda na sama ba ya tausaya wa na kasa, shi ma na kasa din idan an nemi taimaka masa sai ya yi ha’inci.
Abin bukata dai shi ne, mutanen da suke zaune a garurruwan kan iya ba laifi suka yi ba, kaddara ce ta zaunar da su a wuraren, domin haka dole a kula da hakkokinsu kamar kowa, domin haka bai kamata a nemi ganin iyakar mutanen da ke kan iyaka ba.
Kamata ya yi Hukumar Kwastam ta zama mai yaki da fasa-kwaurin tattalin arzikin kasa, ba mai fasa-kwaurin talakawa su kara gurguncewa ba.