Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai kamata ba a ce man fetur ya fi sauki a Najeriya a kan kasar Saudi Arebiya.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya na bikin cika shekara 60 da samun mulkin kai.
“Bai yi ma’ana ba man fetur ya fi sauki a Najeriya a kan Saudi Arebiya” inji shi.
- Kasafin Kudin 2021: An Amince Da Naira Tiriliyan 13.08
- Buhari Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori 4 A Fadarsa
Jawabin na Shugaba Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sasantawa da kungiyoyin kwadago a kan yajin aiki da zanga-zangar da suke yunkurin yi sakamakon karin farashin wutar lantarki da na man fetur.
Buhari ya kuma lissafa kasashe hudu masu arzikin man fetur da ke sayar wa ’yan kasarsu mai a farashi fiye da na Najeriya.
Mafi saukin farashi a cikin jerin kasashen ita ce Saudi Arebiya, wadda take sayar da lita a kan N168.
Sannan akwai Chadi, inda ake sayar da lita a kan N362; da jamhuriyar Nijar, N346; da Ghana, N326; da kuma Masar, N211.
“A wannan yanayi, dole ne gwamnati ta fuskanci gaskiyar halin da ake ciki ta kuma dauki matakin da ya dace.
“Ya kamata a kara farashin man fetur”, inji shi.
“’Yan uwana ’yan Najeriya, idan har muna son cimma burinmu to dole ne mu kara jajircewa, mu kara dagewa, mu kuma bai wa junanmu kwarin gwiwa, don aiwatar da abin da ke daidai ko da zai kasance babu mai ganinmu.”
Kada ku manta za ku iya bibiyar yadda ‘yan Najeriya ke bukukuwan cika shekara 60 da samun mulkin kai a sassa daban-daba na kasar a nan: https://aminiya.dailytrust.com.ng/live.