An tashi ci 2-1 a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Bagulori Old Tamas ta yi da takwararta ta G-Town a Jihar Legas.
Wasan, wanda aka gudanar a filin wasa na makarantar sakandaren unguwar Daji da ke yankin karamar hukumar Agege a jihar an shirya shi ne don sada zumunci a tsakanin kungiyoyin biyu.
Da farko kungiyar kwallon kafa ta G-Town ta rika kai wa kungiyar Old Tamas hari amma daga bisani sai reshe ya juye da mujiya kungiyar Old Tamas ta zura mata kwallon farko a raga.
Ba a yi minti goma ba sai kungiyar G-Town ta farke kwallon da aka zura mata ba tare da bata lokaci ba.
Cikin ’yan mintoci bayan an dawo hutun rabin lokaci ne sai kungiyar Old Tamas ta sake zura kwallo ta biyu kuma har aka tashi G-Town ba ta farke ba.
Kyaftin din kungiyar Bagulori Old Tamas Malam Jibo danyaro Wanzan ya bayyana farin cikinsa da yadda wasan ya gudana.
Malam Jibo ya yabawa ’yan kungiyarsa ta Old Tamas inda ya ce kishi da juriya ne suka sa suka yi nasara a wasan.
Ya yi fatan nan gaba ’yan wasan Old Tamas za su ci gaba da kokari don kai kungiyar gaci.
Da yake jawabi, mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta G-Town, Alhaji Inuwa Ofisa ya bayyana bakin cikinsa dangane da rashin nasarar da suka samu.
Ofisa ya bayyana cewa kungiyarsa za ta sake gayyato Old Tamas domin a sake kece raini a wasa na gaba.
’Yan kallo da dama da Aminiya ta tattauna da su sun yaba wa kungiyar kwallon kafa ta Bagulori Old Tamas dangane da kokarin da suka yi.
Sun bayyana cewa nasarar da kulab din Old Tamas ya samu a kan G-Town ya nuna cewa G-Town tana da sauran aiki a gabanta.
Bagulori Old Tamas ta lallasa G-Town da ci 2-1
An tashi ci 2-1 a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Bagulori Old Tamas ta yi da takwararta ta G-Town a Jihar Legas.Wasan, wanda aka…