✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baffa sak!

Wani mai wasa da biri ne ya shiga kasuwa yana bin rumfuna-rumfuna yana ba su dariya. Duk abin da aka ce birin nan ya yi…

Wani mai wasa da biri ne ya shiga kasuwa yana bin rumfuna-rumfuna yana ba su dariya. Duk abin da aka ce birin nan ya yi sai ya yi, sai kwatsam suka je rumfar wadansu Fulani, sai suka ce wa mai birin: “Ka sa birin nan ya yi mana tafiyar Jauro ya dawo daga gona ya gaji.” Ai kuwa birin nan sai ya yi yadda aka umurce shi, sai daya daga cikinsu ya ce: “Kai aradun Allah Baffa sak!”
Daga Abba Barrister Kano, 08137880496