Majalisar Sarakunan Arewa dake Kudancin Najeriya ta koka kan tsare shugabanta Sarkin Hausawan Lagos Alhaji Aminu Yaro da hukumar DSS ta yi.
Majiyar Aminiya ta ce DSS ta gayyaci Sarkin Hausawan ne tare da mai ɗakinsa dangane da zargin badaƙalar da ake yi wa amininsa dakataccen Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, Godwin Emefiele.
Sai dai sanarwar da Majalisar ta fitar ta hannun Jarman Lagos Yarima Shettima ta ce ba daidai ba ne DSS ta tsare Sarkin da mai ɗakinsa har tsawon kwanaki uku ba tare da gurfanar da su gaban shari’a ba.
Kotu ta ba DSS umarnin sakin Godwin Emefiele
DSS ta gurfanar da Emefiele gaban kotu
Sanarwar ta ce duk da yake Sarkin Hausawan aminin Mr Emefiele ne, abin da DSS ta yi ya keta masa alfarma kuma cin zarafi ga ɗaukacin al’ummar Hausawa mazauna kudancin ƙasar nan.
Sai dai kakakin DSS Peter Afunanya ya shaida wa wakilanmu cewa babu abinda zai ce game da wanann batu.