✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Badala: Hisbah ta kama Daliban Jami’a a Kano

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama wasu dalibai maza da mata su 42 cikin daki daya a Unguwar Dambare daura da Jami’ar Bayero. Danbare…

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama wasu dalibai maza da mata su 42 cikin daki daya a Unguwar Dambare daura da Jami’ar Bayero.

Danbare unguwa ce da yawanci daliban jami’a ke zaman kansu, musamman wadanda ba su son zama cikin jami’a, inda ake zargi bata-gari sun lalata unguwar.

Aminiya ta samu rahoton cewa, a ranar Laraba aka kama daliban samari da ’yan mata da ake zargi suna kwana tare a daki daya, inda aka rankaya da su ofishin hukumar da ke kusa.

Sai dai wani mazaunin yankin, ya ce simamen ya sanya fargaba ta kama wasu daliban da har suka raba dare suna tunanin abin ka iya zuwa ya dawo.

Wannan ba shi ne farau ba da Hisbah take shiga unguwar domin kama wadanda ake zargi da aikata badala inda wasu ke ganin hukumar na amfani da wannan dama ce don cin zarafin wadanda suka samu wani sabani da su.

Wani dalibi mazaunin unguwar wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu yadda suka taba arangama da jami’an na Hisbah.

“Dalibi ne ni kuma bayan na yi aure ba jimawa na fara zuwa Jami’ar Bayero, hakan ya sanya na dawo da mata ta mu ci gaba da zama tate na tsawon lokacin da zan kammala karatun.”

“Haka wata rana suka shigo mana gida ba tare da izini ba, sai daga bisani su gane mu ma’aurata ne,” a cewar dalibin.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Kumbotso, Gwani Murtala, ya ce an tura wadanda aka kama din zuwa Babban Ofishin Hukumar don gudanar da bincike.