✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar Naira Biliyan 165: PDP ta bukaci Buhari ya tsige Ministan Sufuri

Ana zargin badakala da yin sama da fadin fiye da naira biliyan 165 a Hukumar NPA.

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP, ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta tsige Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da Hadiza Bala, Babbar Daraktar Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwan Kasar wato Nigerian Ports Authority (NPA).

PDP ta yi wannan kira ne sakamakon zargin badakala da yin sama da fadin fiye da naira biliyan 165 a Hukumar NPA.

Wata sanarwa da kakakkin jam’iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Litinin, ta yi kira ga shugaban kasar da ya gaggauta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike da gurfanar da kusoshin gwamnatin biyu dangane da zargin.

Kiran da jam’iyyar ta yi na zuwa ne bayan da a makon jiya Shugaba Buhari ya dakatar da Hadiza Bala daga mukaminta, biyo bayan shawarar da Amaechi ya bayar kan zargin badakalar kudaden a hukumar da take jagoranta.

Kazalika, Ministan ya kuma kafa wani kwamiti bincike mai dauke da wakilai goma, domin dubba duk wasu ayyukan shige-da-ficen kudi a hukumar tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Sai dai PDP ta kalubalanci salon Ministan na kafa kwamitin da ya kunshi jami’an ma’aikatarsa domin bincikar lamarin.

Akan haka ne PDP ta yi kira da Buhari ya dakatar da duka su biyu, sannan a mika su ga Hukumar EFCC mai Yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da aka dora wa nauyin gudanar da bincike kan makamanciyar wannan takaddama.

Mista Kola ya ce hakan ne kadai zai bai wa Ministan da Babbar Daraktar NPA damar wanke kansu muddin sun taki gaskiya a lamarin.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa akwai wata makarkashiya da Ministan ke son rufewa, “dalili ke nan da ya sa Ministan bai tashi binciken babbar daraktar ba shekaru shida da suka gabata da ya yi aiki da ita, sai yanzu.”

Sai dai tuni babbar daraktar ta musanta zargin, inda cikin wata wasika da ta aikewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, akwai kuskure a kididdigar kasafin kudin hukumar da na kudaden shigar da take Tarawa.

Haka kuma, ta nesanta kanta da aikata kura-kurai da kudaden shigar hukumar har naira biliyan 165, kamar yadda Ministan ya yi korafi.