Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 14 da aka yanke wa Faisal Maina, dan tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho, Abdulrasheed Maina, bisa laifin hada baki da kuma karkatar da kudade.
Sai dai kuma kwamitin mutum uku na alkalan kotun daukaka karar ya rage wa’adin zaman gidan yarin Faisal Maina daga shekara 14 zuwa bakwai, saboda wannan shi ne karon farko da aka same shi da laifi a kotu.
- Bakin haure 50,000 sun mutu a hanyar neman ingantacciyar rayuwa —IOM
- Dillalan kwaya 993 sun shiga hannu a Katsina
A hukuncin da Mai Shari’a Ugochukwu Ogakwu ya yanke, kotun ta ce Mai Shari’a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yi daidai da ya yanke wa Faisal hukuncin dauri a gidan yari.
Amma a cewarsa, tun da wannan ne karon farko da ya aikata laifi, bai kamata kotun ta yanke masa hukunci mai tsauri ba idan aka yi duba da doka.
A ranar 8 ga watan Oktoban 2021 ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Faisal hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari bayan samun sa da laifin karkatar da kudaden gwamnati.