Ministan Sufuri Mista Rotimi Chibuike Amaechi, ya ce magance matsalar tsaro da kawo ci gaba a fannin ilimi zai sa gaba idan aka ba shi damar zama shugaban kasa a 2023.
Amaechi ya bayyana haka ne a Benin, yayin ganawarsa da masu ruwa da tsakin APC a Jihar, lokacin da ya kai wa Oba na Benin, Ewuare II ziyara a fadarsa, ziyara.
- An yi gwanjon rigar kwallon Maradona kan Naira biliyan 3.6
- Matsalar tsaro: Buhari, gwamnonin Arewa da shugabannin tsaro sun sa labule
Amaechi, ya ce shi ne ya fi dacewa wajen dawo da Najeriya kan turbar daidai da zarar ya dare mulki a 2023.
“A lokacin da na ke gwamnan Jihar Ribas wadannan matsaloli biyun, su na fi mayar da hankali ne kai, sai kuma sufuri, hanyoyi da noma, zan yi irin wannan idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa”.
A nasa bangaren, Oba Ewuare II, ya bukaci Amaechi ya yi addu’a ga ubangiji don neman biyan bukatunsa.
Ya kuma bukace shi da kada ya manta da sarakunan gargajiya da masu zabe musamman matasa, ya kara da cewa ya kamata a bai wa matasa damar kawar da tashe-tashen hankula a lokutan yakin neman zabe.
Sarki ya koka kan yadda masu rike da mukaman siyasa musamman gwamnoni ke yi wa sarakunan gargajiya rikon sakainar-kashi, ba su nemansu sai lokacin zabe ya zagayo